Majalisar Ɗinkin Duniya ta ba da sanarwar janye jami’anta daga Somaliya.
October 13, 2006Talla
Majalisar Ɗinkin Duniya, ta ce ta ɗau matakan janye duk jami’anta baƙi daga wasu yankuna na Somaliya, bayan an yi musu barazanar kisan gilla. Wata sanarwar da jami’an majalisar suka bayar a birnin Nairobin Kenya, ta ce wannan matakin dai na wucin gadi ne. Amma ba su bayyana ko wane ne ke yi wa jami’an a Somaliya barazanar kisa ba, sai dai sun ce suna ɗaukar barazanar da muhiimanci. Mayaƙan ƙungiyoyin islama ne dai ke riƙe da mafi yawan yankunan kudancin Somaliyan a halin yanzu.