Birtaniya: Jajiberin barin EU
January 30, 2020Talla
A yayin da yake karbar bakoncin sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo a birnin London, primiyan Birtaniyan zai yi kokarin gabatar da hanyoyin masalaha kan sabanin da ke tsakanin bangarorin biyu kan kasuwanci, tattaunawar da ke zuwa gabanin cikar wa'adin ficewar London daga EU a gobe Juma'a.
Da matsayin Birtaniyar a wani wadi na tsaka mai wuya a tarihi, Johnson na kokarin cimma yarjejeniyar kasuwanci da Kungiyar ta EU da kuma Amurka a daya hannun, duk kuwa da koma bayan "dangantaka ta musamman" da ke tsakanin London da Washinton, a baya bayannan.