Makomar Somaliya bayan zaben shugaban kasa
September 10, 2012'Yan Somaliya ne dai ke saye da sayar da kayan lambu da sauran kayan bukatun yau da kullum a Unguwar Eastleigh da ke birnin Nairobin Kenya. Hasali ma dai ya na daya daga cikin wuraren da suka mamaye tun bayan da suka kaurace ma kasar ta Somaliya sakamakon yaki da ta ke fama da shi. Duk ma dai da Zaben 'yan majalisa da ma dai na shugaban kasa da aka gudanar, bai sa 'yan Somaliya da ke da zama a kenya sha'awar komawa kasarsu ta asali ba. Maimakon haka ma dai, hada guywa suke yi domin kafa kananan masana'antu ciki kuwa har da Hotel. Abubakar Sheikh Ali, wanda daya ne daga cikin wadanda suka zuba hannu jari wajen gina hotel "Ben Ali" mai dakunan 114 a Nairobi ya ce al'amarin kafa masana'antu a Mogadischo na ba su tsaro.
"Muna da wani katafaren hotel a Mogadischu, wanda sojojin kasar Habasha suka ragargaza lokacin yaki. Muna so mu sake gina shi. Amma muna ganin cewar bakin alkalami ya bushe saboda al'amura ba su daidaita a Mogadishu ba."
Baya ga Kenya dangin shi Ben Ali na neman kudi ne a kasashen Djibuti da Somaliland da Sudan ta kudu da kuma Uganda. Sun juya ma kasarsu baya ne saboda hasarar kudi da ya kai miliyon 16 na dollar Amirka da suka yi a inda baya ga hotel, suka asarar dukkanin kadarorin da suka mallaka a Mogadischu. Duk da cewa an zabi shugaban mai cikakken iko a wannan rana (10 ga watan satumba 2012). Amma dai Abubakar sheikh Ali ya ce wannan mataki bai zai zai inganta halin rayuwar talakawa ba matikar gwamnati ba ta farka daga barci ba.
"Zaman lafiya ba zai samu a Mogadischu ko ma dai Somaliya ba sai idan mutane sun samu ayyukan yi maimakon dogaro da aikin sojan sa kai wajen samun kudin shiga. Wannan ya na nufin cewar akwai bukatar kafa masana'antu domin a samu guraben aiki. A halin yanzu kashi biyar ko 10% ke da aikin yi. Sauran kashi 95% na fama ne da zaman kashe wando. A wannan yanayi ba abin mamaki ba ne, matsalar tsaro ta ci gaba da zama karfen kafa."
Akasarin 'yan Somaliya da ke gudun hijira na danganta zaben 'yan majalisa da na shugaban kasa da ci gaban mai hakon rijiya. Shi ma Emmanuel Kisangani jami'i a cibiyar nazarin al'amuran tsaro da ke mazauninta Nairobin Kenya, ya ce cin hanci da karbar rashawa na ci gaba da tasiri a yunkurin da ake yi na mayar da Somaliya kan kyakkyawar turba.
"Mambobin gwamnatin wucin gadi sun tsaya takara a matakai daban daban domin su ci gaba da kakkange madafun iko. Saboda haka wuka da nama na hannun jami'an gwamnati mai ci a yanzu. Alhali suna cikin manyan jami'an da aka zarga da cin hanci da kuma karbar rashawa."
Duk da yankar kauna da al'uma suka nuna musu, tsofoffin masu fada a ji na gwamnatin Somaliya sun yi amfani da dukiyarsu wajen samun mukami. Ko da a zaben kakakin majalisar dokokin na Somaliya da ma dai na shugaban kasa, sai da masu gida rana suka taka rawar gani.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Yahouza sadissou Madobi