Man fetir alheri ko akasin haka a Nijar
November 30, 2017Hakikan bayan kwashe shekaru shida da kafuwa a yankin Jihar Damagaram tare da fara aikin tatar mai gadan-gadan jama'a daga masu ababen hawa zuwa 'yan farar hula na ci gaba da bayyana ra'ayoyi game da ribar da suka ci ta mai da kuma kamfanin tace man kasar mai sunan SORAZ baki daya, sun ce dai ba su ga canji ba saboda tsada gara ma lokacin da ba a tace man.
Tun bayan kafuwar kamfanin tace man ne dai 'yan farar hular irin su MPCR suka fara gwagwarmayar ganin sai an rage farashi amma dai har yanzu babu ci gaba, ga gurbata muhalli.
A shekarun baya dai manyan motocin dakon mai na 'yan kasuwa ne da kuma gwamnati ke shigo da man daga ketare, su ma dai sun ce babu aiki, faduwa suke kawo yanzu. A na su waje kungiyoyin da ke sa ido a kan ma'adinai irin su GREEN na ganin dai har yanzu akwai sauran aiki kafin kaiwa ga nasara baki daya.