1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manyan labaran Afirka da suka fito a jaridun Jamus

December 23, 2022

Mika wa Najeriya kayan tarihi da zaman sojojin Jamus a Nijar da siyasar Afirka ta Kudu da ma rikicin yankin Tigray na Habasha, sun dauki hankalin jaridun Jamus na mako.

https://p.dw.com/p/4LNIl
Hoto: dpa

Za mu fara sharhin na yau ne da jaridar Die Zeit a sharhinta mai taken: "Tafiya ta farko a tarihi. A karshe an mayar wa da Najeriya tagullarta da aka dauko daga birnin Benin." Jaridar ta ce yanzu lokaci ya yi, akwatuna dauke da Tagullar Benin na farko cikin jirgin daukar kaya tare da ministar hakokin kasashen waje ta Jamus Anna­lena Baer­bock da takwararta ta al'adu Claudia Roth sun tashi daga filin jirgin sama na Berlin fadar gwamnatin Jamus, zuwa Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya. Sama da shekaru 10 ke nan da fara zazzafar muhawara kan yadda ya kamata a yi da kayan tarihin da Turawan mulkin mallaka suka sato daga kasashen Afirka da suka mallake. Jamus ta yanke shawarar dinke baraka ta hanyar mayar da kayan tarihin. Bayan tattaunawa tsakanin ma'aikatar raya al'adun Najeriya da Jamus, cikin watan Yuli ministar harkokin kasashen wajen Jamus da takwaranta na Najeriya sun sanya hannu kan yarjejeniyar mayar da Tagullar ta Benin. Jamus ta sha gaban sauran kasashen Turai wajen daukar wannan mataki, tare kuma da tallafawa jihar Edo wajen gina gidan adana kayan tarihin da za a ajiye kayan da aka dawo da su.

Ziyarar shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a Nijar
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Sojojin Jamus sun fadada zamansu a Nijar, in ji jaridar Neues Deutschland. Jaridar ta ce bayan da rundunar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar Tarayyar Turai ta kawo karshen zamanta a Mali, sun ya da zango a mawakbciyar kasa. Ta ce kasashe mambobin kungiyar Tarayyar Turai, sun amince da bayar da sabon tallafi ga sojojin Jamhuriyar Nijar. Jamus za ta jagoranci makamancin wannan tsari ga 'yan sanda, kuma za su yi aiki tare da rundunar nan ta Frontex. Ministar harkokin tsaro ta Jamus Christine Lambrecht ta sanar da cewa, nan gaba kadan Jamus din na shirin aikewa da karin sojojinta zuwa Nijar karkashin tsarin hadin gwiwa na dakarun kasashen kungiyar Tarayyar Turai EU a Nijar din wato EUMPM. Ministar ta kuma bayyana cewa, gwamnatin Jamus za ta gina asibitin sojoji ga Nijar din.

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung ta rubuta sharhinta ne mai taken: "Shugaba Ramaphosa na Afirka ta Kudu ya tsallaka mataki na gaba, duk da zargin cin hanci da rashawa, shugaban kasar ya ci gaba da rike mukamin shugabancin jam'iyyar ANC mai mulki. Jaridar ta ce kanwa ta kar tsami kwarnafi ya kwanta ga Cyril Ramaphosa bayan da ka sake zabarsa a matsayin shugaban jam'iyyar ANC mai mulkin Afirka ta Kudu, yayin babban taron jam'iyyar da ta gudanar a birnin Johannesburg.

ANC | Shugaba Cyril Ramaphosa
Hoto: Denis Farrell/AP Photo/picture alliance

Mai shekaru 70 a duniya, ya sha mamaki lokacin da ya ji magoya bayansa na taya shi murna. A yanzu dai, Ramaphosa zai ci gaba da zama mutum mai muhimmanci a Afirka ta Kudu, domin ba dan sake zabarsa a matsayin shugaban ANC din ba zai yi wahala ya ci gaba da zama a kujerar shugaban kasa. Duka mukaman biyu, mutum guda ke rike su. Hakan na nuni da cewa nan da tsawon wasu shekaru biyar masu zuwa, jam'iyyar ta sake damka amanarta da ma ta kasar ga mutumin da ake zargi da boye makudan kudi da yawansu ya kai dalar Amirka dubu 580 a gidan gonarsa. Sai dai kuma, jam'iyyar ba ta da wani wanda ya fi shi a yanzu.

Za mu karkare da jaridar Der Tagesspiegel a sharhinta mai taken: "Rikicin Tigray, daukar nauyin yakin da kudin mazauna ketare. Jaridar ta ce: Tun bayan samun 'yancin kanta, Iritiriya ke cin karenta babu babbaka da kudin haraji daga 'yan kasarta mazauna ketare. Da wadannan kudi take daukar nauyin yakin da ta shiga kane-kane a yankin Tigray da ke arewacin makwabciyar kasa Habasha. A hukumance tun daga biyu ga watan Nuwambar da ya gabata aka daina barin wuta, a yakin na tsawon shekaru biyu da aka bayyana da mafi muni a duniya. Dakile karbar haraji daga mazauna kasashen ketare, zai taimaka wajen magance rikicin.