Karin albashi ga kananan ma'aikata a Nijar
July 12, 2023Talla
A baya dai kasar ta Nijar ce a sahun baya a jerin kasashen UEMOA mai karamin albashi na Smigue wanda à yanzu ta kara shi zuwa jaka 42 na Cefa.
A tsakiyar makon farko na wanan watan ne dai ta bakin Dokta Ibrahim Bukari da ke zaman ministan ma'aikatan kwadagon kasar ta kafar sadarwar kasa ya ayyana karin kudin a kan albashin kananan ma'aikata da ake kira da SMIG, da a yanzu ya tashi jaka 42, karin da ba tun yau ba kungiyoyin ma'aikatan kwadago ke faman ganin ya tabbata.
Tsarin karin kudi ga masu kananan albashi, shugaban kasa da kansa ne ya dauki wannan aniya inda ya baiyana wa shugabannin kungiyoyi, domin a inganta rayuwar ma'aikata da halin da ake ciki dangane da matsi na tattalin arzikin kasa.