1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin EU akan harin ƙunar baƙin wake a Somaliya

August 25, 2010

Ƙungiyar Tarayar Turai(EU) ta yi Allah wadai da harin da ya auku a Mogadishu

https://p.dw.com/p/Ovdw
Catherine Ashton, kantomar ƙungiyar EU kan manufofin ƙetare.Hoto: AP

Kantomar Ƙungiyar Tarayyar Turai(EU) kan manufofin ƙetare, Catherine Ashton ta yi Allah wadar da harin 'yan tawaye da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 31 a Mogadishu babban birnin ƙasar Somaliya. Daga cikin waɗanda suka mutun har da wasu 'yan majalisar dokokin ƙasar. Wani ɗan bindiga daga ƙungiyar al-Shabaab ne ya yi sojan gona da da sojan gwamnati, kana ya auka ma wani ginin otel inda ya yi musayar wuta da jami'an tsaro kafin ya tayar da bom da ya ɗaure a jikinsa. Ashton ta kira wannan hari tamkar abin da sam ba za a amince da shi ba, tare da bayyanar da alhinin Ƙungiyar Tarayyar Turai(EU) ga al'umar Somaliya. Komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma jami'ai daga Amirka su kuma sun la'anci wannan hari. Wannan harin dai ya auku ne kwana biyu bayan ɓarkewar wani kazamin faɗa, da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 70 a birnin na Mogadishu.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Abdullahi Tanko Bala