1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masalaha a rikicin juyin mulki kasar Burkina Faso

Mohammad Nasiru AwalSeptember 25, 2015

A wannan makon ma dai jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne a kan kasar Burkina Faso, inda a ranar Laraba gwamnatin rikon kwaryar kasar da wasu sojojin suka hambarar, ta koma kan mulki.

https://p.dw.com/p/1GdoC
Michel Kafando
Hoto: picture-alliance/dpa/E. Rogard

A labarin da ta buga jaridar Die Tageszeitung cewa ta yi kafin ya sake mika ragamar mulki, sai da jagoran masu juyin mulkin Gilbert Diendere ya aiwatar da aikin shugaban kasa, inda ya tarbi wakilan kungiyar ECOWAS da suka je kasar don bikin sake mika mulkin. Jaridar ta ce a wani kwarkwaryar biki a fadar gwamnati da ke birnin Ouagadougou, Shugaban riko Michel Kafando ya ba da sanawar komawarsa kan kujerar mulki, mako guda bayan da sojojin da ke gadin fadar shugaban kasa da kuma ke zama na kurkusa da tsohon shugaban kasar Blaise Compaore suka yi juyin mulki.

Bukatun al'umma sun rinjaye na 'yan juyin mulki

Masu juyin mulki a Burkina Faso sun mika kai ga bukatun al'umma sun kuma kuduri aniyar komawa barikokinsu, inji jaridar Neue Zürcher Zeitung.

Burkina Faso Unruhen in Ouagadougou
Hoto: Reuters/J. Penney

Ta ce sa'o'i 24 bayan alamun tabarbarewar halin da ake ciki a Ouagadougou babban birnin kasar Burkina Faso, a ranar Laraba hankali ya kwanta a rikici tsakanin jagoran masu juyin mulki Janar Gabriel Diendere da rundunar dakarun da ke biyayya da dokokin kasar. Jaridar ta ce hankali ya kwanta kwana guda bayan an sanya hannu kan yarjejeniyar da ta tanadi kwance damarar sojojin da ke gadin fadar shugaban kasa. Shi kuma a nasa bangaren Janar Diendere ya mutunta kiran da kungiyar tarayyar Afirka AU da kuma ECOWAS suka yi na ya janye daga fadar shugaban kasa ya ba wa wanda dokar kasa ta amince da zama ciki wato shugaban rikon kwarya Michel Kafando. Jaridar ta yaba da yadda aka kawo karshen wannan rikicin ba tare da an zubar da jini ko digo daya ba.

Tsarin sufuri na zamani ga jama'ar gari

Jirgin kasa na zirga-zirgar jama'a cikin gari a kasar Habasha, har wayau dai inji jaridar Neue Zürcher Zeitung tana mai mayar da hankali kan wani gagarumin aikin layin dogo a birnin Addis Ababa don saukaka wa jama'a zirga-zirga zuwa harkokinsu na yau da kullum a babban birnin na Habasha.

Äthiopien erste Straßenbahn in Addis Abeba
Kokarin zama na farko wajen shiga jirgin karkashin kasa a Addis AbabaHoto: DW/Y. Gebreegziabher

Ta ce a birnin Addis Ababa an bude layin dogo na zamani kuma na farko a wata kasar Afirka Kudu da Sahara, wanda kasar Sin wato China ta samar da kudin gininshi. Kasancewa babban birnin na kasar ta Habasha kamar sauran manyan biranenn kasashen Afirka, ana fama da cunkoson ababan hawa, wannan sabon tsarin sufurin fasinja da kananan jiragen kasa, zai kawo saukin zirga-zirgar jama'a, da habaka harkokinsu na kasuwanci da kuma bugu da kari rage yawan gurbata muhalli daga hayakin motoci.

Yarjejeniya tsakanin EU da Afirka ta Yamma

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung labari ta buga game da takaddama a majalisar dokokin Jamus kan wata yarjejeniya tsakanin Tarayyar Turai EU da wasu kasashen yammacin Afirka.

Ta ce tun bayan sanya hannu kan yarjejeniyar Cotonou da ta tanadi inganta huldar cinikaiya tsakanin kungiyar EU da kasashen yammacin Afirka, wani gungun wakilan majalisar dokoki ta Jamus ke yi ta tayar da jijiyar wuya saboda ba a tabo maganar kare muhalli da kuma 'yancin kananan yara ba. Suka ce dole sai an nemi amincewar majalisar. Yanzu haka dai batun na gaban kotun kundin tsarin mulkin kasa.