1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara ba wa mata lasisin tukin mota a Saudiyya

Zulaiha Abubakar MNA
June 4, 2018

Saudiyya da ke aiki da dokokin Musulunci tsantsa ta fara ba wa mata lasisin tuki biyo bayan sauye-sauye da Yarima mai jiran gado ke aiwatarwa.

https://p.dw.com/p/2yvfL
Saudi-Arabien Riad Aziza al-Yousef
Hoto: picture-alliance/AP Photo/H. Jamali

Gwamnatin kasar Saudiyya ta fara rabawa mata lasisin tukin mota kamar yadda babbar kafar yada labaran kasar ta sanar a wannan Litinin.

Sanarwar ta kara da cewar a halin yanzu  hukumar kula da ababen hawa a kasar ta fara maye gurbin shaidar tukin da ta amince da ita a baya da lasisin tuki duk dai a cikin shirye-shiryen bai wa matan kasar izinin tuka mota wanda za a kaddamar a ranar 24 ga watan Yunin wannan shekara.

Wannan dai shi ne karo na farko a tarihin kasar ta Saudiyya da mata za su fara tuka mota bayan fara halartar filayen wasan motsa jiki tun bayan bijiro da sabbin canje-canje da Yarima Muhammad bin Salman ya fara gudanarwa.