Mata sun fara tuki a Saudiyya
June 25, 2018Talla
Duk da cewar tun kafin zuwan wannan rana, an bude tarin cibiyoyin koyar da matan tuki, sai dai da dama daga cikin wadanda suka samu lasisin na da zumudin da suke da shi na yin tukin suna jin tsoron karo ko samun hatsari. Ana dai sa ran tukin matan zai kawo karuwar matan da za su dinga fita aiki, kamar yadda zai karya kasuwar sana,ar tukin da maza ke yi wa matan kasar. Duk hakan dai na zuwa ne, a daidai lokacin da matan da suka yi ta fafutukar ganin an bai wa matan na Saudiyya yancin tuki dama kawo sauyi na hakika a kasar ke can garkame gidan yari, kan sukar masarautar da suke yi.