1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan cimma kyakkyawan Shugabanci a Somaliya

May 2, 2013

Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kudirin agazawa Somaliya domin cimma burin shugabanci na-gari.

https://p.dw.com/p/18QyZ
(From L-R) Portuguese ambassador to the United Nations Jose Filipe Moraes Cabral, Russian ambassador to the United Nations Vitaly Churkin and South African ambassador to the United Nations Baso Sangqu vote during a Security Council meeting at the United Nations in New York April 21, 2012. The U.N. Security Council unanimously adopted a resolution on Saturday that authorizes an initial deployment of up to 300 unarmed military observers to Syria for three months to monitor a fragile week-old ceasefire in a 13-month old conflict. REUTERS/Allison Joyce (UNITED STATES - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

A wannan Alhamis ne kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya yi zaman daya yanke shawarar tallafawa gwamnatin Somaliya ta hanyar aza ginshikan tabbatar da zaman lafiya game da baiwa gwamnatin kasar shawarwarin da za su kai ta ga wanzar da shugabanci na-gari a tsakanin al'umma. Kudirin da mambobin kwamitin sulhun suka yi na'am da shi - da murya guda, ya tanadi samar da hukumar da za ta kula da wadannan batutuwa ne a farko farkon watan Yuni, wadda kuma a mataki na farko, za ta gudanar da ayyukanta cikin wa'adin watanni 12.

Daga cikin abubuwan da hukumar, za ta baiwa gwamnatin Somaliya shawara harda bullo da manufofin da za su gina kasa, da shirye shiyen gudanar da zabuka a shekara ta 2016, da mutunta dokokin da suka shafi jin kan bil'Adama da kuma tabbatar da kawo karshen muzgunawa jama'a - ta hanyar take hakkiinsu.

Tuni dai kungiyar kare hakin bil'Adama ta Human Rights Watch, tare da hukumomin bayar da agaji suka yi marhabin lale da wannman matakin da kwamitin sulhun na Majalisar Dinkin Duniya ya dauka.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab Mohammed Abubakar