Matakan kasada da Kenya ta ɗauka a Somaliya
November 4, 2011A wannan makon ma dai kamar a makon jiya, maganar kutse sojojin Kenya a Somaliya ita ce ta mamaye kanun rahotannin da jaridun Jamus suka gabatar akan nahiyarmu ta Afirka. A cikin nata rahoton jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi:
"Sojojin Kenya sun kutsa kai a kudancin Somaliya, amma kuma bata san ƙarashen lamarin ba. Domin kuwa ko da Kenyar ta samu nasara kan ƙungiyar Al-Shabab ta kuma fatattaki dakarun ƙungiyar daga sansaninsu a Kismayu mai tashar jiragen ruwa a gaɓar tekun Indiya, ba za a iya cewar fadar mulki a Nairobi ta cimma wata takamaimiyar nasara ba, matsawar da ba a haɗa matakin sojan da wani mataki na siyasa domin cike giɓin da zai samu a kudancin Somaliya ba."
Ɗaruruwan mutane suka yi asarar rayukansu sakamakon wata sabuwar arangama da ta kunno kai a yankin tsaunukan Nuba dake Sudan kuma dukkan gwamnati da 'yan tawaye na zargin juna da laifin zub da jini a yankin kudancin Kordofan. Jaridar Die Tageszeitung ce ta rawaito wannan rahoton ta kuma ƙara da cewar:
"Rikicin ya fi yin tsamari ne a lardin kudancin Kordofan da kuma lardin Blue Nile dake kusa da iyaka da Habasha. Kuma ganin yadda fadan ke daɗa yin tsamari da wuya a samu kusantar juna tsakanin sassan da ba su ga maciji da juna a wannan rikici ya ƙi ci ya ƙi cinyewa."
A wata harkar kasuwanci dake samun bunƙasa ba ƙaƙƙautawa, lamarin da jaridar Die Zeit ke gani tamkar wata mummunar taɓargaza ce, ana cinikin gwanjon riguna da Jamusawa ke bayarwa kyauta ga wasu ƙungiyoyin taimako masu zaman kansu, a kasashen Afirka, inda jaridar ta ce akan sayar da kowane kilo daya na tufafin akan dalar Amirka ɗaya da cent ashirin a ƙasar Kongo. Jaridar ta ce wani abin takaici game da haka ma dai shi ne yadda waɗannan tufafin ke kassara harkar saƙe-sa-ƙe a nahiyar Afirka. A ƙasar Tanzaniya kawai mutane kimanin dubu tamanin suka yi asarar guraben ayyukansu sakamakon taɓargazar cinikin tsaffin tufafin daga Jamus.
A can Ghana kuwa tsaffin kayan lantarki da ake kaiwa ƙasar daga nahiyar Turai ne ke barazana ga makomar lafiyar jama'a da ma kewayen ɗan-Adam a kasar, kamar yadda jaridar Die Tageszeitung ta rawaito. Jaridar ta ce wani abin lura game da wannan mummunan ci gaba shi ne kasancewar ainihin sinadaran dake barazana ga lafiyar jama'a daga kayayyakin lantarkin da suka yi kwantai a ƙasar ta Ghana, galibi sun ƙunshi wasu muhimman ɗanyyun kayayyaki, waɗanda ake nemansu ruwa a jallo a kasuwannin duniya, amma yawansu bai kai yadda za a iya cin gajiyarsu ta fannin tattalin arziƙi ba. A sakamakon haka duka-duka abin da yara da matasa ke iya fitarwa daga tsaffin kayan lantarki shi ne tagulla, kuma abin da xya rage sai a ƙona, inda hayaƙin ke barazana ga lafiyar jama'a dangane da abubuwa na guba da ya ƙunsa.
Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal
Edita: Umaru Aliyu