Matakan sassanta rikicin siyasar Nijar
March 22, 2016
Batun ci gaba da bayar da sakamakon zaben da aka yi mai tattare da hayaniya da ma matsayin 'yan adawa na kauracewa zaben kwata kwata da ake ganin ke shirin shigar da kasar ta Nijar a cikin wani mawuyacin hali, na cigaba da daukar hankali.
Manya-manyan hukumomin kasashen waje dauko daga na Majalisar Dunkin Duniya har zuwa ga Tarayyar Turai da Tarayyar Afrika da ma wasu masu fada aji daga kungiyoyin masu zaman kansu, da suka saka ido a zaben da kuma yanzu hakan suke bibiyar yanda matsayin Nijar yake duba da barazana da ke fitowa walau daga 'yan adawa ko kuwa daga bangaren masu rinjaye.
Sai dai matakin kin aminta da zaben tun ba'a bayar da sakamakonsa ba da wallafa adadin wadanda suka ce su ne kawai suka fito jefa kuri'a a zaben mai tattare da hayaniya, ya kasance abinda wakilin sakataren Majalisar Dunkin Duniya ya fi damuwa da shi tare da dubo hanyoyin sake maido da masalaha a tsakanin bangarorin da basa ga maciji.
Ta dalilin haka ne ma ya sa wakilin ya yi wata ganawa da bangarorin biyu na adawa da na masu rinjaye a yammacin jiya don ganin bangarorin sun yayyafawa zukatansu ruwan sanyi
Mohamed Ibn Chambas ya ce" na zo ne don ganawa da shugabannin 'yan adawa don duba yanda MDD za ta iya samar da masahala dangance da wannan yanayi na kiki-kaka da ke addabar kasar a ga ta yanda majalisar za ta iya yin wani dan abu dangance da wannan halin. Daga farko lalle kam mun ga zaben ya kasance da daukacin 'yan takara to amma kuma sai dai a zaben zagaye na biyu mun lura da cewar babu daya dan takarar kuma 'yan adawa sun kira da a kaurace masa. Wannan kuwa ga MDD abu ne mai kyau don muga mun ci gaba da tattaunawa da bangarori dan samo bakin zaren warware matsalar ta a cikin ruwan sanyi".