Matashin da ya koma Afirka daga Turai
July 6, 2022Pharrel Abraham Djollo mai shekaru talatin ya bar kasarsa ta haihuwa Cote d'Ivoire samakakon rikicin da ya biyo bayan zaben 2011, inda ya je Faransa don neman ilimi da koyon sana'a. Ya fara koyon sana'ar fassarawa da hada murya a finai-finai, kafin ya je Ghana da Najeriya don ya inganta Ingilinsa, sannan ya ya da zango Maroko inda ya samu aikinsa na farko.
Pharrel ya yii aiki a matsayin mai fassarar zanen ban dariya na yara a kan albashi kusan Yuro 2,000 a kowane wata, ma'ana sama da miliyan daya da dubu dari biyu da arba'in da hudu na kudin CFA. Amma sha'awarsa ta aikin kansa da kawo sauyi a fannin fina-finai ya sa shi komawa Côte d'Ivoire don kafa kanfaninsa mai suna Abidjan Dubbing Avenue.
Karin Bayani: Sabon salon gidan abinci a Senegal
"Kafin in fara wannan aikin, na fara tuna Cote d'Ivoire. Mun kallon fina-finan Najeriya da fina-finan Amirka, a nan Côte d' Ivoire. Kuma lokacin da na je Ghana da Najeriya, ban ga wani fim na 'yan Côte d Ivoire ba. Don haka na yi yunkurin tallata abubuwan da muka iya yi a Côte d' Ivoire. Don haka na yi tsarin yadda aikin zai gudana kuma na neman kudin gudanar da aikin. Na fara ne lokacin da aka yi fama da Corona, saboda komai ya tsaya cik a Turai, a nan ne na yanke shawarar komawa Côte d'Ivoire."
Komawa birnin Abidjan ke da wuya, sai Pharrel Abraham Djollo ya kaddamar da kasuwancinsa tare da daibar matasa maza da mata aiki. Amma ya fuskanci kalubale sakamakon rashin tallafi. hasali ma, kudin haya ya wau Pharrel Djollo, lamarin da ya kashe masa gwiwa
"Ba samu wani taimako daga hukuma ba. Farashin kayan aiki don fara wannan kasuwancin na da tsada sosai. Amma tanadi da na yi tun da farko ya sa na sayi duk abin da nake bukata a matsayin kayan aiki. Yana da matukar wahala. Wannan ya zama kalubale a gare mu. Mun ta fadi tashi amma ba mu sami manyan abokan ciniki ba. Amma ina da kwarin gwiwa. Ina kokarin sabunta fasaha don cimma burin da na sa a gaba."
Karin Bayani: HdM: Mai na'urar ba wa fanka caji
Duk da wahalhalun da ya fuskanta, Pharrel Abraham Djollo na dogara ga abokinsa David Kouadio, wanda ya shafe shekaru bakwai yana yin fassarar da kuma dora murya a fina-finai. Kwarewar Pharrel Abraham Djollo na karfafa wa sauran matasan Afirka gwiwa kamar su Joliane Noity da Joyce Tokré daga Cote d'Ivoire, wadanda ske samun horo a kanfanin Abidjan Dubbing Avenue, inda ta ce "Ni 'yar kasar Benin ce, na zo nan ne don a horar da ni. Don haka ina yabawa."
Don kada ya yi nadama rungumar wannan sana'an, Pharrel Abraham na gudanar da kananan kasuwanci don samun karin kudin shiiga, tare da kula da mijigi, baya ga aikin inininya a kafafen rediyo da talabijin. A yanzu haka ma Pharrel Abraham shirin horarwa a makarantu don koyar da wannan sana'a ga kananan yara manyan gobe.