Mathias Sorgho dan tseren keke a Burkina Faso
December 23, 2015Shahararriyar gasar tseren kekuna ta kasa da kasa da aka fi sani da Tour du Faso, gasa ce da ake gudanarwa tun a shekara ta 1987 wacce ke shigen Tour de France koda yake ba ta kaita armashi ba, yanzu haka dai daruruwan masu tseren Afrika ne ke taka rawa a wannan gasar. Mathias Sorgho dan Burkina Faso ne da ke da burin tsallakawa Turai don taka rawar da ka iya zama abin kwaikwayo ga 'yan Burkina Fason,
Mathais Sorgho, na kan hanyarsa ta cika burinsa na kasancewa dan kasar Burkina Faso na farko wajen shahara a harkokin gasar tseren kekuna, hakan ya sanya shi sadaukar da kansa da lokacinsa wajen shiga tseren gasar kekuna mafi girma da aka fi sani da suna Tour de Faso wanda daga karshe ya zamo na uku.
"Ina ganin wannan sakamakon mai kyau ne, a gaba daya ma dai wannan shi ne karon farko da na shiga gasar, burina shi ne na cigaba da taka rawa da sauran masu fafatawar. Mutane a nan sun ji dadin yadda na zama na uku a gasar kuma nima ina murna da abin da na yi".
Dogon burin Sorgho a cikin sana'ar tsren kekeuna
Dan tseren mai shekaru 24 a duniya ya fara tinkarar atisaye shekaru biyu da suka wuce, yanzu haka na cikin tawagar babbar kungiyar Burkina Faso kuma tuni ya sami nasarar tseren a kasar Benin, to amma tseren Tour de Faso ana matikar cin kwakwa bisa la'akarin maki 40 na yanayin zabi a ma'aunin Celsius, masu tseren dai su kan shafe gudun kilomita 1000.
"Akwai wahala, ba ka iya samun lokacin yin abubuwan da kake so misali fita shakatawa da abokaina, a harkar tsere dole ka tabbata ganin ka ci abinci yadda ya dace tare da samun hutu sannan ka kwanta bacci don tashi da wuri".
Laurent Bezault da ke zama daraktan tseren Tour de Faso na ganin Sorgho yana da duk wani abu a tattare da shi wajen samun nasarar tsallakewa don samun tsallakawa kasashen duniya. Bezault a karan kansa ya taba shiga gasar Tour de Faso.
"Kwarrare ne a gasar kuma yana daukar wasanin da matukar mahimanci, to amma yana bukatar tallafin kudade da horaswa, idan ya samu likafarsa zata yi gaba sosai".
Kalubalen da ke a gaban Sorgho a cikin tseren kekuna
Sorgho shi kansa yana da masaniyar cewar yana da kalubale a gabansa muddin yana son cimma burinsa na kasancewa shahararre, da farko yana bukatar keke mai kyau, a yanzu haka yana amfani da keken kungiyarsu ne.
"Harkar tana lakume kudade kafin a ce ka zama fitaccen dan tseren keke a wannan lokacin, dole ne ka nakalci duk abubuwan dake da alaka da tseren keke wajen kasancewa fitaccen magujin keke".
A Burkina Faso Sorgho da danginsa tuni suka fara tattauna dabaru a nan gaba yayin da yake fatan komawa Jami'a to amma a cikin zuciyarsa tuni ya tsinci kansa a matsayin shahararren dan tsere a da'irar masu tseren nahiyar turai.