Ta'addanci
Najeriya: Matsalar 'yan gudun hijira
November 2, 2022Talla
Kungiyar ta Human Rights Watch ta bayyana haka ne cikin wani rahoto da ta fitar ta ce 'yan gudun hijirar sun shiga halin taskun ne, bayan da gwamnati ta rufe wasu sansanoninsu tare da hana kungiyoyin agaji kai musu dauki. Cikin watan Oktobar shekarar da ta gabata ta 2021 ne gwamnatin jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriyar kana makyankyasar kungiyar 'yan ta'addan ta Boko Haram da ta addabi Najeriya da makwabtanta, ta sanar da rufe dukkan sansanonin 'yan gudun hijira da ke dauke da dubban mutane tare kuma da mayar da wasunsu garuruwansu na asali.