Matsalar bala'in yunwa a Somaliya na ƙara bazuwa
August 4, 2011Ƙwararrun masana na Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin Nairobin ɗin Kenya, sun yi gargaɗin cewa taimakon da ake ba wa al'umomin ƙasashen yankin ƙahon Afirka masu fdama da matansanciyar yunwa, ba zai wadatar ba. A dangane da mawuyacin halin da ake ciki a yankunan dake fama da matsalar fari, yanzu haka an ayyana ƙarin yankuna guda uku a Somaliya da cewa wurare ne da wani bala'i ya afka ma. Yanzu haka dai yawan mutanen dake fama da matsananciyar yunwa ya ƙaru musamman a kudanci da kuma tsakiyar Somaliya mai fama da yaƙin basasa. Hakazalika yawan waɗanda ke mutuwa sakamakon rashin abin sakawa bakin salati ya ƙaru. A Somaliya kaɗai mutane miliyan 3.7 ne ke fuskantar barazanar masifar yunwa. Akan haka ƙungiyar tarayyar Afirka ta kira wani babban taron ƙasashe masu ba da tallafi a ƙasar Ethiopia, a ƙoƙarin daƙile raɗaɗin wannan matsala.
Mawallafi: Nasiru Salisu Zango
Edita: Ahmad Tijani Lawal