1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar Fari na cigaba da addabar al'ummar Somaliya

July 16, 2011

Gwamnatin kenya zata bude ƙarin wani sansanin 'yan gudun hijira a kan iyakar ta da Somaliya domin taimakawa masu guduwa daga matsanancin farin Somaliya

https://p.dw.com/p/11wgX
Hoto: Bettina Rühl

Sabon sansanin wanda ke Arewa maso gabashin Kenya zai iya daukar kimanin mutane dubu 80. Ana sa ran wannan sabon sansanin dai zai rage cunkoson da ake fama da shi a sansanin Dadaab wanda ke zama sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a duniya, inda ma'aikatan agaji na majalisar dinkin duniya suka ce a yanzu haka kimanin mutane dubu 439 ke samun mafaka.

Kungiyoyin agaji sun yi kiyasan cewa akalla mutane milliyan 10 ke fuskantar barazanar yunwa kuma MDD ta yi gargadin cewa bata da isashen kudin da zata iya amfani da shi wajen tallafawa wadanda abun ya shafa.

A wani labarin kuma Jamus ta ribanya tallafin da ta baiwa masu gudun hijira dga Somaliya zuwa Kenya sakamakon Fari. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sake alkawarin tallafin euro milliyan 5 zuwa yankunan da masu aikin agaji suka ce na fuskantar barazanar yunwa. Ministocin bada agaji da na harkokin wajen Jamus sunce zasu raba tallafin tsakanin kungiyoyin agajin Jamus da na kasa da kasa da kuma hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya. A ziyarar da ta kai Kenya, Merkel ta sanar da tallafin euro milliyan daya zuwa ga sansanonin 'yan gudun hujiran wanda kuma rabin kudin zai shiga aljihun hukumar abincin na duniya.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Ahmed Tijani Lawal