1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar 'yan gudun hijirar Somaliya

July 14, 2011

Dubban-dubatar 'yan gudun hijira ke kwarara zuwa ƙasar Kenya sakamakon bala'in fari da yunwar dake addabar maƙobciyar ƙasa ta Somaliya

https://p.dw.com/p/11vSl
'Yan gudun hijirar Somaliya dake kwarara zuwa KenyaHoto: dapd

A dai halin da ake ciki yanzu miliyoyin mutane daga ƙasashen gabashin Afirka da suka haɗa da Somaliya da Kenya da Ethiopia da Djibouti da Uganda waɗanda tuni suke fama da rikice rikice sun faɗa wani mawuyacin hali sakamakon bala'in fari. A cikin wata sanarwa da ta fitar hukumar kula da 'yan gudun hijra ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce a watan Yunin da ya gabata kaɗai an samu mutane dubu 54 da suka ƙaura daga ƙasar ta Somaliya waɗanda kimanin 1400 daga cikinsu suka kwarara zuwa sansanonin 'yan gudun hijra dake garin Dadaab na arewacin ƙasar Kenya.

Za iya cewa duk wanda ya samu nasarar isa wannan wuri ya tsira daga wahala. A kowace rana ta Allah ana samun kimanin 'yan gudun hijra dubu biyu dake kwarara zuwa wannan sansani da gwamnatin Kenya ta kafa a garin Dadaab. Fatuma mai 'ya'ya uku na daga cikin waɗanda suka shafe makonni suna tafiyar ƙafa kafin sun tsallaka zuwa ƙasar Kenya.

"A can gida muna da dabbobi kuma mun bukaci a ba mu fili. Dukan raƙummanmu da shanunmu da awakinmu sun halaka kuma ƙasa ta kame babu ruwa a cikinta. Ba mu kuma da ƙarfin yin cefane saboda tsadar kayan abinci."

A dai sansanin akwai katin da ake bai wa Fatuma da take amfani da shi domin samun abinci na ƙwarai da ta daɗe tana rashinsa. A kudancin Somaliya ana fama da rashin ruwan sama. Kuma ma'aikatan ba da agaji suna ɗari ɗarin zuwa wannan yanki saboda da kasancewarsa ƙarƙashin ikon ƙungiyar Alshabab. A dai baya bayan nan lamarin ya kassance babu wanda ke tsira da ransa in har yayi kutse zuwa wannan yanki. A jefi-jefi 'yan bindiga su kan bukaci a kawo kayan abinci ko kuma sauran dangogin taimako. To amma ƙungiyoyin ba da agaji ba su lamunta da su ba a cewar Fafa Attidza jami'in aikin kula da yan gudun hijra na Majalisar Ɗinkin Duniya.

"A dai halin yanzu muna nazarin hanyar samar da abinci a cikin gaggagwa. Hakan ne dai zai rage yawan mutane dake ratsawa zuwa cikin ƙasar Kenya. To amma ba zamu iya zuwa Somaliya ba har sai zarafi ya ba mu damar yin hakan."

Hungersnot in Kenia
Makiyaya na Somaliya sun yi asarar dabbobinsu sakamakon fariHoto: Picture-Alliance/dpa

Wannan kuwa taimako ne da ake matuƙar buƙatarsa a cikin aƙalla makonni biyu. In ba haka ba za a samu ƙarin mutane da zasu ƙaura daga ƙasar ta Somaliya. Za a kuma fuskanci ƙarancin abinci a sansanonin 'yan gudun hijrar.

"Za a fuskanci matsala in har aka ci gaba da fuskantar wannan hali zuwa wata uku ko huɗu. Ba zamu iya samar da taimakon abinci da ruwa da magunguna da kuma wurin barci ga mutane kusan dubu 35 a kowane wata har ya zuwa gaba da watanni huɗu ba."

Da farko an gina sansanin 'yan gudun hijrar na garin Dadaab ne domin ɗaukar mutane dubu 90. Amma a wasu lokaci ana samun mutane dubu 400. Da yawa daga cikinsu suna kwana ne akan 'yan filayen dake tsakanin itatuwa . Sauoda Mohammed na ɗaya daga cikin yan gudun hijirar.

"Ba mu da komai in banda tufafin da muke saye da su. Muna buƙatar tantuna saboda matsanancin sanyi da ake yi da daddare."

Ban Ki Moon Pressekonferenz New York
Ban Ki Moon lokacin taron manema labarai a New YorkHoto: Picture Alliance/Photoshot

Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya dai yi kira da a ba da ɗauki sakamakon matsalar yunwar da ake fuskanta a Somaliya da kuma halin rashin tabbas da 'yan gudun hijirar ke tsintar kansu a ciki. Ga baki ɗaya dai sakataren na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce ana buƙatar Euro sama da miliyan dubu domin taimaka wa mutanen dake yankin ƙahon Afrika.

Mawallafi: Antje Diekhans/Halima Balaraba Abbas

Edita. Ahmad Tijani Lawal