1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar yunwa ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a Somaliya

August 12, 2011

A baya ga yunwa a Somaliya jaridun Jamus sun yi nazari kan matsalar dagwalon man fetir a Najadelta da kuma manufofin China dangane da Afirka

https://p.dw.com/p/12Fj5
Gurɓacewar koguna a yankin NajadeltaHoto: picture alliance/dpa

Har yau dai mawuyacin halin da ake ciki a ƙasar Somaliya shi ne ya fi ɗaukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus, ko da yake jaridar Süddeutsche Zeitung tayi bitar matsalar yankin Najadelta dangane da maganar dagwalon man fetir da ya lalata muhallin yankin. Jaridar ta ce:

"Bisa ta bakin shugaban Najeriya Goodluck Jonathan dai ɓarnar da dagwalon man fetir ke wa muhalli ta zarce raɗaɗin da kan biyo bayan wani yaƙi na basasa. Wani rahoton da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar baya-bayan nan kuwa sai da ya tabbatar da cewar haƙan mai a yankin Najadelta bai haifarwa da al'umar yankin wadata ba sai dai annoba da matsaloli na rashin lafiya da gurɓacewar muhalli. Manyan kamfanoni na ƙetare kuma su ne ke da alhakin wannan mummunar ɓarna a cewar rahoton kuma wajibi ne su ɗauki nauyin tsaftace wa al'umar yankin muhallinsu."

Har yau talakawan dake zaune a yankunan dake ƙarƙashin ikon ƙungiyar nan ta Al-Shabab a ƙasar Somaliya na ci gaba da fama da raɗaɗin yunwa sakamakon ci gaba da ƙiyawa ƙememe da ƙungiyar ke yi na kai musu taimakon abinci. A lokacin da take gabatar da rahoto game da haka jaridar Berliner Zeitung cewa tayi:

Hungersnot in Somalia
Sansanin 'yan gudun hijira a MogadishuHoto: dapd

"A wani mataki mai kama da hangen haske daga nesa, a karon farko a cikin shekaru biyar da suka wuce, wani jirgin sama mai ɗauke da kayan taimako da suka haɗa da barguna da tantuna da makamantansu na ƙungiyar taimakon 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ya sauka birnin Mogadishu. To sai dai kuma raba kayan taimakon ya ta'azzara saboda barazanar da jami'an taimakon ke fuskanta, ba ma daga dakarun Al-Shabab kaɗai ba, har ma da dakarun sa kai na sassa da ba sa ga maciji da juna da kuma sojojin gwamnatin wucin gadi dake famar wawason kayan taimakon. Dangane da yankunan dake ƙarƙashin ikon Al-Shabab kuwa, inbanda ƙungiyoyin taimako na musulmi da ƙungiyar red cross ta ƙasa da ƙasa da ta likitoci da kuma ƙungiyar Unicef ba a amince da taimako daga wata ƙungiyar dabam ba."

Gwamnatin Jamus tayi Allah waddai da manufofin China dangane da nahiyar Afirka, a cewar jaridar Die Tageszeitung. To sai dai kuma kamar yadda jaridar ta nunar Chinar tayi fatali da zargin da ake mata na ma'amalla da ƙasashen nahiyar ta hanyar da ba ta dace ba. Maganar dai ta shafi ƙorafin da ƙasashen Turai ke yi ne na cewar China na sayen filayen noma a ƙasashen Afirka, lamarin da gwamnati a fadar mulki ta Bejing ta ce faufau ba ta taɓa sayen fili a Afirka ba. Chinar dai duk da cewar tana cikin jerin ƙasashe masu tasowa, amma tana ba wa ƙasashen Afirka taimakon raya ƙasa kuma daga baya-bayan nan ta yafe wa ƙasashen nahiyar rancen kuɗin da ya kai Euro miliyan dubu biyu kuma bisa ga ra'ayinta, wai ƙasashen na yammaci na zargin Chinar ne domin su kawar da hankalin jama'a daga ainihin kurakuran da suka caɓa a wannan nahiya.

Landraub in Kambodscha
Ana zargin China da sayen filayen noma a AfirkaHoto: Thomas Kruchem

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita:Umaru Aliyu