Sabon hari ya kashe sojojin Burkina Faso
April 22, 2021Talla
Rahotanni daga Ougadugu babban binrin kasar Burkina Faso na cewa akalla sojoji hudu sun mutu wasu 12 sun jikkata a wani harin kwantan bauna da mahara dauke da manyan makamai suka kaddamar.
Kasar Burkina Faso na cikin kasashen yankin Sahel da ke fuskantar barazanar mayakan jihadi tun bayan da suka kaddamar da kai hare-hare a kasar Mali a shekarar 2015.