Kisan ma'aitakan sa kai a Burkina Faso
April 15, 2021Harin ya auku ne a lokacin da ma'aikatan ke aikin tsaro na sinitiri a yanjkin arewacin kasar.
Maikatan sun bi sahun wasu barayi dabbobi ne da suka yi awon gaba da busashe a lokacin da 'yan bindigar suka hallakasu a Siguidi kusa da lardin Gorasdi
A shakarar 2019 ne aka kafa wannan kungiya ta VDP da zummar taimakawa jami'an soji yaki da mayakan da ke gwagwarmaya da makamai, amma suna fama da munanan hare-hare a lokuta da dama wanda tun daga shekara bara kawo yanzu aka kashe sama da mutum 200 daga cikinsu.
Ire-iren wadannan hare-haren a kan farafen hula da masu bada agaji na kara karuwa a koda yaushe wanda a 'yan kwanakin nan, Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da kwashe ma'aikatanta daga shiyar arewa maso gabashin Najeriya bayan wani hari a offishinsu.