1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hujjoji sun danganta bin Salman da kisan khashoggi

Gazali Abdou Tasawa
June 19, 2019

Wasu hujjjo masu karfi da aka fitar a rahoton bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun danganta yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya Mohammed Bin Salman da hannu a kisan Jamal Khashoggi.

https://p.dw.com/p/3Kjo6
Bildkombo Saudi-Arabien | Jamal Khashoggi & Mohammed bin Salman

Wata kwararrar jami'ar Majalisar Dinkin Duniya ta zargi yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya Mohamed Bin Salman da ba da umurnin kashe Jamal Khashoggi shahararren dan jaridar nan dan asalin kasar ta Saudiyya da aka kashe a karamin ofishin jakadancin Saudiyya a Turkiyya a ranar biyu ga watan Oktoban shekarar 2018. Ta yi wannnan zargi ne a cikin rahoton bincike da ta gabatar inda ta kuma bukaci a gudanar da wani binciken kasa da kasa kan rawar da yariman ya taka a cikin wannan kisa.

Watanni shidda kwararrar jami'ar Majalisar Dinkin Duniya Agnes Callamard ta share tana gudanar da bincike kan kisan dan jaridar wanda ya yi kaurin suna wajen caccakar mahukuntan kasar ta Saudiyya, binciken da ta ce ya kai ta  kasashe da dama musamman Turkiyya. Sabanin binciken da kasar Saudiyya da kuma wasu kasashen na daban suka yi kan batun kisan dan jaridar inda suka mayar da  hankali kan sanin su wa suka aiwatar da kisan, Jami'ar Majalisar Dinkin Duniya Agnes Callamard ta ce binciken nata ya mayar da hankali ne kan neman sani wa ya ba da umurnin kisan dan jaridan, lamarin da ta ce ya ba ta damar samun hujjoji da suka sa take kyautata zaton cewa akwai hannun Yarima Mohamed Bin Salman wajen bada umurnin kisan dan jaridar.

Istanbul Agnes Callamard Sonderberichterstatterin willkürliche Hinrichtungen
Agnes Callamard mai bincike ta MDDHoto: picture-alliance/AP/C. Yurttas

"Ta ce ba ni da hujjoji na zahiri kan wa ya ba da umurnin aikata kisan, amma hujjojin da na mallaka na nuni da cewa akwai yiwuwar da hannun wasu shugabanni na koli na kasar ta Saudiyya. Amma akwai bukatar zurfafa bincike musamman kan Yarima Mohamed Bin Salman a bisa dalillai masu yawa, kuma daya daga cikin dalilan shi ne mutanen da ke da hannu dumu-dumu wajen aiwatar da kisan dan jaridar"

Jami'ar Majalisar Dinkin Duniyar ta kuma bayyana cewa ta la'akari da hujjoji masu karfi da ke da akwai a yanzu kan zargin rawar da Yarima Bin Salman ya taka wajen kisan dan jaridar akwai bukatar saka sunansa a jerin mutanen nan 17 da kasar Amirka da wasu manyan kasashen duniya da suka dauki mataki ladabtarwa kansu :

"Ta la'akari da hujjojin da suka ba da damar gudanar da wannan bincike na kasa da kasa , shi ya sa na ga ya dace a saka shi cikin jerin mutanen da aka saka wa takunkumi, matsawar ba a samu wasu sabbin hujjojin da ke nuni da cewa ba shi da hannu a ciki kuma bai da masaniya kan kisan ba"

Istanbul Saudischer Journalist Khashoggi betritt Konsulat von Saudi-Arabien
Khashoggi a ofishin jadakancin Saudiyya a TurkiyyaHoto: Reuters TV

Callamard ta kuma yi kira ga mahukuntan kasar ta Saudiyya da su dakatar da shari'ar da suke yi wa wasu 'yan kasar su 20 wadanda mai shigar da kara ya bukaci yanke wa biyar daga cikinsu hukuncin kisa bayan sun wanke Yarima Bin Salman daga zargin kisan dan jaridar.

"Ta ce ina da shakku mai yawa kan zaman shari'ar kansa domin a tashin farko mutane 20 aka kama, amma kuma 11 kawai aka tuhuma. Kuma babu wasu dalillai da aka bayyana kan dalillan kin tuhumar sauran mutanen tara. Kuma da akwai alamar boye wata gaskiya a cikin shari'ar, dan haka ina ganin babu abin da zai sa in dauki wannan shari'a a matsayin sahihiya"

Tuni dai mahukuntan kasar ta Saudiyya ta bakin ministan harkokin wajenta Abdl al-Jubeir suka yi watsi da sakamakon wannan bincike wanda suka ce ba shi da tushe balantana makama. Sai dai kuma wani babban abin lura kan wannan batu shi ne kusan tsawon yini guda bayan gabatar da wannan rahoto da ya yi zargi mai karfi kan kasancewar hannun Yarima Bin Salman a kisan dan jarida Jamal Khashoggi, har yanzu shiru kake ji daga bangaren  kasashenTurai da Amirka wadanda bisa al'ada ke yin azarbabin bayyana matsayinsu da ma daukar mataki a irin wannan lamari.