1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Meles Zenawi shugaba mai fuskoki biyu

August 24, 2012

Kasashen Habasha da Afirka ta kudu da Somalia suna daga cikin wadanda suka dauki hankalin jaridun Jamus a wannan mako

https://p.dw.com/p/15w2O
Hoto: AP

To jaridun na Jamus da dama sun maida hankalinsu kan mutuwar Pirayim ministan Habasha, Meles Zenawi a farkon wannan mako, wasu kuma sun yi nazarin yajin aikin ma'aikatan hakar Platinum a Afrika ta kudu, inda sakamakon dauki ba dadi, muitane dfa yawa suka rasa rayukan su, sai kuma halin da ake ciki a Mali da Somaliya.

Jaridar Tagesspiegel ta duba mutuwar Pirayim ministan Habasha, Meles Zenawi a farkon wnanan mako. Tace kafin mutuwar sa Zenawi ya kasance mutumin da ya tabbatar da kwar-kwaryar zama lafiya a kahon Afirka, yankin da rikici ya zama ruwan dare a cikin sa. Tun daga yan makonnin da suka wuce aka fara rade-radi a game da makomar sa, to amma duk lokacin da aka sami wani labari game da rashin lafiyar sa, nan da nan gwamnati a Addis Ababa takan musunta haka. Jaridar Tagesspiegel tace Zenawi mutum ne mai fuskoki biyu. Ta fuskar siyasa, ya hana abokan adawar sa zaman lafiya, wanda a tsawon mulkin kama karya da yayi na tswon shekaru 21, ya kasa samun kwarin gwiwar aiwatar da canje canje na siyasa, amma a bangaren tattalin arziki, ya taimaka ba ma ga ci gaban Habasha kadai ba, amma har ga samun bunkasar yankin kahon Afirka.

Jaridar Berliner Zeitung tayi sharhi a game da kisan da aka yiwa ma'aikatan hakar Platinum a Afirka ta kudu, inda tace wannan mummunan abu, babu wanda za'a dora laifin hakan a kansa, in banda shugaba Jacob Zuma. Jaridar tace kisan da jami'an tsaro suka yiwa ma'aiakatan a lokacin da suke zanga-zangar neman kyautata sharuddan aikin su, abin da ya hada har da karin albashi, ya tunatar da zamanin mulkin wariyar jinsi, inda bakar fata aka rika kashe su kamar dabbobi. Sakamakon dauki ba dadin tsakanin jami'an tsaro da yan zanga-zanga, akalla mutane 36 ne aka kashe a wurin hakar ma'adinin na Platinum mallakin kamfanin Lonmin a Marikana. Kungiyar ma'aikatan hakar ma'adinai ta Afirka ta kudu a takaice, tace wannan tashin hankali zai zama mai muhimmanci ga makomar Afirka ta kudu.

Südafrikanischer Bergarbeiterstreik Gewalt und Tote in Marikana
Yan sanda sun dakace masu zanga-zanga a Afirka ta kuduHoto: Reuters

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung tayi sharhi ne a game da dage zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a Somaliya ranar 20 ga watan Agusta. Shugaban kwamitin dattijai a sabuwar majalisar da aka zaba a makonnin baya, yace an dage zaben ne saboda rashin kammala tsarin da ya dace. Hakan dai ya kai ga cewar Somalia yanzu bata da shugaban kasa na hakika, saboda wa'adin shugaban rikon kwarya, Sheriff Sheikh Ahmed tun ranar da aka shirya zaben ya cika. Ko da shike shugaban mai barin gado shi ake sa ran zai sake lashe zaben idan aka yi shi, amma akwai yan takara a ciki da wajen kasar, da suka hada har da tsoffin shugabanni Mohammed Ali da Hassan Sheikh Adam. A watan Agusta na bara ne aka kara wa'adin gwamnatin ta rikon kwarya a Somaliya da shekara guda, inda kungiyoyi da kasashen da suka fi baiwa Somaliyan taimako suke matsa lambar samun ci gaba a bangaren siyasa a kasar, yayin da suke kira ga rundunar AMISOM ta kungiyar hade kan Afrika ta kara matsa kaimi a yakin ta kan dakarun al-Shbaab da suka haka Somaliya zaman lafiya.

Jaridar Tageszeitung ta tabo shari'ar da ake yiwa wasu yan Kongo biyu a birninStuttgart na nan Jamus, bisa zargin su da aiyukan rashin imani karkashin kungiyar yan tawaye ta FDLR a gabashin kasar. Kotun yana tuhumar mutanen biyu ne da laifuka har 65, ciki har da wadanda suka shafi yaki 39. Mutanen biyu, Murwanashyaka da Musoni, an zarge su da kashe mutane akalla 214 da fyade akalla 15 da kuma laifukan daukar kananan yara aikin soja.

Somalia Präsident Abdullahi Yusuf Ahmed
Shugaban rikon kwarya na Somaliya Abdullahi Yusuf AhmedHoto: CHRIS YOUNG/AFP/Getty Images

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Abdullahi Tanko Bala