Michel Kafando ya sha ranstuwar kama aiki
November 18, 2014Shugaban Burkina Faso na rikon kwarya Michel Kafando ya ce gwamnatinsa za ta mutunta tsarin dimokradiya a kasar kana za ta yi bakin iyawarta wajen ganin lamura sun daidaita.
A wani jawabi da ya yi bayan da ya sha rantsuwar kama aiki dazu, Mr. Kafando ya ce yanzu haka idanun al'ummar kasar a bude suke don haka ba zai yiwu a cigaba da tafiya a irin doron da ake yi a baya ba.
A jiya Litinin ce aka dai aka zabi Kafando don jagorantar gwamnatin rikon kwarya bayan da tsohon shugaban kasar Blaise Compaore ya yi murabus sakamakon matsin lamba da zanga-zanga da jama'ar kasar suka rika yi.
A gobe Laraba ce dai ake sa ran shugaban zai nada firaminista wanda za su hada gwiwa da shi wajen zaben mutane 25 da za su yi aiki da su a majalisar ministocin kasar.