Taron ministocin EU a karon farko tun bayan corona
July 13, 2020Talla
Ministocin Turan da dama sun bayyana rashin jin dadinsu kan inda gwamnatin Shugaba Recep Tayyip Erdogan ta dosa, da matakinta na mayar da wurin tarihi na Hagia Sophia zuwa masallaci, kasar da har yanzu ke fafutukar shiga kungiyar ta EU.
Taron ministocin tarayyar Turan 27 da ke zama irinsa na farko na keke da keke a birnin Brussels tun bayan bullar corona, na nazari kan dangantakar kungiyar da Turkiyyar.
Turan dai na zargin Ankara da saba yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya na hana sayarwa Libiya makamai, ta hanyar goyon bayan gwamnatin Tripoli da ke da amanar Majalisar Dinkin Duniya.