1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhimmancin nahiyar Afirka wajen samun tsaro a Turai

Mohammad Nasiru AwalApril 14, 2016

Ana gudanar da taron Munich kan sha'anin tsaro a Addis Ababa inda aka bayyana muhimmancin Afirka kan samun tsaro a Turai.

https://p.dw.com/p/1IW9b
Münchner Sicherheitskonferenz in Addis Abeba
Wolfgang Ischinger (a dama) a taron birnin Addis Ababa kan tsaroHoto: DW/G.Telda HG

A wannan Alhamis aka bude taron kwanaki biyu kan lamuran tsaro da aka saba yi a birnin Munich na nan Jamus, amma a wannan karon ana taron ne a birnin Addis Ababa na kasar Habasha. Kimanin mahalarta taro daga kasashe dabam-dabam na Afirka da Turai da Amirka suke halartar taron da ke mayar da hankali kan manufofin tsaro na kasa da kasa. A wani taron manema labarai, Ambasada Wolfgang Ischinger da ke zama shugaban taron tsaro na birnin Munich ya ce Turai ta fara gane muhimmancin Afirka idan ana maganar tsaro.

"Yanzu a Turai mun fara gane cewa Afirka na da muhimmanci. Ba kamar a da ba lokacin da aka mayar da hankali kan batutuwan tallafin raya kasa, ko da yake har yanzu suna da muhammanci, amma batun tsaron yana da muhammanci ga Afirka da Turai baki daya."

Shi ma ministan tsaron Habasha Tedro Adhanom ya ce sabanin a da, yanzu tasirin matsalolin Afirka ba su tsaya a nahiyar kadai ba, suna yaduwa a wasu nahiyoyi.