Mummunan harin kunar bakin wake a kudancin Somaliya
August 22, 2015Talla
Harin dai ya wakana ne a cikin wani gina na Jami'a da ke kauyen birnin Kismayo, inda dakarun kiyaye zaman lafiya na kasar Kenya na AMISOM da ke karkashin inuwar Tarayyar Afirka da kuma na kasar ta Somaliya suke. Wata karamar sapa ce dai shake da bama-bamai ta tarwatse a sashen motsa jiki na sojojin inda nan take sojoji 14 suka rasu tare da jikkata a kalla 20 a cewar Mohamed Abisalad, jagoran sojojin na Somaliya a birnin Kismayo, sannan kuma shaidun a babban asibitin birnin sun tabbatar da wannan adadi.