Murabus ɗin Firimiyan Japan
June 2, 2010Talla
Firayim ministan ƙasar Japan Yukio Hatoyama ya sanar da cewa zai ajiye aikinsa, watanni tara bayan kama aiki. Firimiyan dai yana fiskantar matsin labba daga jam'iyarsa, da sai ya sauka gabanin zaɓen 'yan majalisar dattawan ƙasar da za'a gudanar a watan gobe. Gwamnatinsa ta samu koma baya daga shawa'awar da 'yan ƙasar ke mata, tun bayan kama mulki a bara. Inda 'yan ƙasar ke cewa dama ya yi musu alƙawarin rufe sansanonin sojin Amirka dake tsibirin Okinawa, amma yakasa yin hakan, abinda kuma ya jawo masa mummunan baƙin jini.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu