Murna ta koma ciki ga makiyaya a Somaliya da Habasha
Kokari da burin makiyay a Somaliya da Habasha na watanni shida na samun ruwan sama da ciyawa ga dabbobinsu ya ci tura, kuma barazana babba ga dabbobinsu da ma tsarin rayuwarsu.
Takaicin makiyayi
“Abun damuwa ne har yanzu, ina kokarin kwantar wa da kaina hankali a cewar Mohammed Noor mai shekaru 40. Kamar sauran makiyayan Habasha a yankin Somaliya, ya yi tafiya mai nisa zuwa gabar ruwan Somaliland bayan samun labarin ruwan sama da ciyawa mai kyau. Amma ruwan ba yawa, ba zai ishi dabbobin ba." Yanzu awaki 30 ne suka rage masa daga cikin 100. Rakuminsa daya ya mutu biyu kuma suna nan.
Damuna ta zo a makare
Yanzu makiyaya su na komawa gida Habasha, azabar tafiyar hawainiya a hamadar kasar Awdal a yankin Somaliland. Dabbobin da kyar suke tafiya saboda sun galabaita . Wasu dabbobin sun fadi saboda gajiya yayin da wasu kamar wadannan suka mutu, sakamakon sanyi bayan saukar ruwan sama da ya zo a makare. Fari ya kashe dabbobi fiye da miliyan guda a wannan yanki.
Idan ka rasa abun hawa
Abdullahi Amir mai shekaru 70 ya kasance yana da rakuma uku a baya, yanzu wani ramamme ne guda daya ya rage masa. ”Mun kafe a nan, rakumina da ba shi da lafiya ba zai iya daukar komai ba," a cewar Abdullahi da 'yan kayayyakinsa zube a kasa. Abdullahi na tare da mutum hudu daga cikin iyalansa, sauran biyar kuma su na yankin Siti a Habasha. Da aka tambayi menene shirinsa na gaba ya ce: "za mu jira."
Kwararrun matafiya
Ya dauki wadannan iyalai kasa da mintuna biyar kacal su dora kayansu da duk abin da suka mallaka a kan rakuma: Buhunan hatsi da jarkoki da kwalaben man girki da suturu da kuma wata roba da za a shimfida a kan itatuwa domin yin rumfa. Bayan tabbatar da komai ya dauru tsaf, iyalan sun fara tattaki ta kudanci zuwa Ethiopia.
Mallakin rayuwa
Makiyaya na son 'yar karamar akuya. Kan iyaka tsakanin Somaliland da Djibouti ba shi da wani tasiri sosai ga makiyayi a yankin kahon Afirka. Da zarar sun bar gari, su na tafiya duk inda suka ga dama, suna neman ciyawa ga dabbobinsu masu daraja da ke samar musu abun da suke bukata a rayuwa. Dabba daya alama ce ta tanadin da mutum ya yi na abun da ya mallaka a rayuwa.
Karshen tafarkin rayuwarsu
Ana tafiya da garken shanu ta yankin Awdal na Somaliland zuwa Habasha. Kusan ko ina a gabar ruwan Somaliland ramuka ne da aka binne gawarwakin dabbobi. Wasu makiyayan sun rasa dabbobi kimanin 500, tamkar dai tafarkin rayuwarsu ce ta kare. Ragowar dabbobin sun yi rauni yadda ba za su iya tafiya ba, mai yi wuwa a kara rasa wasu dabbobin. Haka dai lamarin ke ci gaba da wakana.
Kowa na da rawar da zai taka
Rayuwa a irin wannan yanayi, kowanne mutum a dangin makiyaya yana da muhimmiyar rawar da zai taka. Yara maza su na daukar fatanyu, akwai na yara yadda za su iya taimakawa wajen sarar itace bayan an gama tattaki na wannan rana an kafa rumfar da iyalan za su zauna.
Zaman dole
Makiyayan da ke zaune a Somaliland su ma fari ya shafe su. Da dama daga cikinsu sun koma yin noma da kiwo inda suka zauna a wuri guda suka kafa tanti na din-din-din. Baderi Adam yana tsaye a kofar gida tare da wasu 'ya'yansa a kauyen Magaalo Xayd, a yankin Gabiley da ke gabashin Awdal. Shekaru 20 da suka wuce iyalinsa sun yi irin wannan zirga-zirga amma yanzu sun daina.
Sabuwar rayuwa?
"Har yanzu akwai wasu makiyayan da suka yi nasara sosai, inda ake cinikin dabbobi masu yawa a hanyar zuwa Djibouti, to amma masu karamin karfi suna rasa dabbobinsu saboda fari da talauci," a cewar John Graham shugaban kungiyar Save the Children ta kasar Habasha. A saboda haka babbar tambayar ita ce yadda za a samar wa musamman matasansu wani aikin na daban.
Wanene ke da hakkin kula da makiyaya?
Ta yaya makiyaya ke jure wa yanayi mai wuyar sha'ani? Kuma wanene ke da alhakin kula da su a yayin da suke tsallaka kan iyakoki daga wata kasa zuwa wata? Akwai bukatar gwamnatoci a yankin su kara tattaunawa da juna a kan wannan, a cewar Abdirashid Haji shugaban yankin Somali na kungiyar taimakon jin kai ta kasa da kasa
Takaicin makiyayi
“Abun damuwa ne kwarai, har yanzu ina kokarin kwantar wa da kaina hankali a cewar Mohammed Noor mai shekaru 40. Kamar sauran makiyayan Habasha a yankin Somaliya, ya yi tafiyar daruruwan kilomita zuwa gabar ruwan Somaliland bayan samun labarin ruwan sama da ciyawa mai kyau. Amma babu ruwan da yawa, ba zai ishi dabbobin ba. Yanzu Awaki 30 ne kacal suka rage daga cikin 100 da Mohammed ya mallka. Rakuminsa daya ya mutu biyu kuma sun rayu."