1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawan Musulmi ya karu a majalisar Amirka

Abdullahi Tanko Bala GAT
January 4, 2019

Ilhan Omar haifaffiyar Somaliya, mai shekaru 36 a duniya, ta zama daya daga cikin mutane biyu Musulumi na farko da suka zama 'yan majalisar dokokin Amirka.

https://p.dw.com/p/3B3O5
Bildergalerie US Wahlen Sieger und Verlierer Ilhan Omar
Ilhan Omar Musulma 'yar asalin Somaliya 'yar majalisar dokokin Amirka Hoto: Reuters/E. Miller

Ita dai Ilhan Omar ta wacce ta je kasar Amirka a matsayin 'yar gudun hijira tun tana 'yar karama ta tsaya takara ne daga jihar Minnesota a karkashin inuwar jam'iyyar Democrats. An zabeta da gagarumin rinjaye inda ta sami kashi 78 cikin dari na kuri'iun da aka kada.

Ta zama 'yar gudun hijira ta farko da ta zama 'yar majalisar dokokin Amirka, kuma mace bakar fata ta farko da za ta wakilci jihar Minnesota a majalisar dokokin a Washington. Bugu da kari mace ta farko da za ta sanya hijabi a cikin majalisar dokoki. Hijaban da Ilhan Omar ke sanyawa masu launukan ruwan toka ko shudi a wasu lokutan baki sukan sa masu sukarta gunaguni. Wasu kalamai na shagube da wasu suka rubuta a shafinta na Instagram cewa tana so ta cusa dokoki irin na Shakira, wato wai Shari'ar Musulunci da kuma faifan bidiyon mawakiya shakira da aka sa hotonta da na Ilham ba su harzuka ta ba, ta cigaba da yin al'amurranta ba tare da damuwa ba.

Ilhan Omar
Ilhan Omar Musulma 'yar asalin Somaliya 'yar majalisar dokokin Amirka Hoto: picture-alliance/abaca/Minneapolis Star Tribune/M. Vancleave

Ilhan ta mayar da martani a shafin Twitter sanye da hijabi tana cewa a yanzu haka majalisar dokokin Amirka za ta kasance sai hakuri. Ilhan dai ta shiga majalisar dokoki kuma jam'iyyarta ta Demokrats na son sauya tsohuwar dokar shekarar 1837 wadda ta haramta sanya hijabi ko alamar addini a majalisa. Ilhan dai ta yi maraba da wannan mataki. Ta ce sanya hijabi bayyanawa ce ta tafarkin addinin da mutum ya yi imani da shi kuma kundin tsarin mulkin Amirka ya ba da kariya a kan haka. Ta bayyana cewa za ta kara azama wajen ganin an sauya irin wadannan haramcin.

Ilhan Omar ta jaddada cewa za ta kalubalanci manufofin Donald Trump a kan 'yan cirani. Sanye da hijabai Ilhan ta fita daban a cikin wakilai 435 a majalisar dokoki. Ilhan ta kasance cikin matasa sabbin jini da ke haskawa a jam'iyyar demokrats. Tuni ma dai shigarta majalisar dokokin Amirka ta fara kawo sauyi.