1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da cin zarafin Musulmi a Turai

Christoph Strack MAB/LMJ
July 13, 2021

Saboda barazana da Musulmi ke fuskanta a Turai, masana daga majalisar Turan da ke yaki da kyamar Yahudawa da Musulmi ke son fuskantar matsalar gadan-gadan da ba da da shawarwari ga 'yan siyasa.

https://p.dw.com/p/3wQnx
Österreich Wien Moschee | Gebet, Trauer nach Terroranschlag
Musulmi na fuskantar karuwar barazana da kyama a TuraiHoto: Leonhard Foeger/REUTERS

Al'ummar Musulmi a Turan dai, na fuskantar barazana da cin zarafi da nuna kiyayya da suka zarta kima. Imam A. yana magana tare da ajiyar zuciya, a lokacin da ya bayyana harin da aka kai a Masallacinsu da ke wani karamin gari a yammacin Jamus, inda ya ce a shekarun da suka gabata wani ya zana kalaman batacin a bangon gidansu. Wannan malamin addinin da bai so a bayyana cikakken sunansa ba, ya kiyasta cewa yawan hare-haren da kiyayya ga Musulmin sun ninka sau da dama a baya-bayan nan. Tsangwama ga Musulmai ya zama wani bangare na rayuwar yau da  kullum a Tarayyar Jamus, kamar yadda Yahudawa ke fuskanta.

Kyamatar Musulmi na karuwa

Alkaluman da ma'aikatar cikin gidan kasar ta fitar, sun nunar da cewa an samu laifuka 1026 na kyamar Musulumci a Jamus a shekarar 2020. Ba dai a Jamus ne kawai Musulmi ke fuskantar karuwar kiyayya da barazana musamman a kafar Internet ba, har ma da sauran kasashen Turai. Daniel Höltgen da ke zama wakilin musamman a majalisar Turai da ke kula da kyamar Yahudawa da Musulmi, ya binciki matsalar kiyayya da kalaman batanci a kungiyoyin Musulmi na kasashen Turai guda takwas. A cikin rahoton sharar fage da ya fitar, yawancin kungiyoyin sun nemi hukumomi su kara matakan kariya da suke dauka.

Daniel Höltgen Sonderbeauftragter des Europarats für Antisemitismus und Muslimfeindlichkeit
Daniel Höltgen dan majalisar Tarayyar TuraiHoto: Christoph Strack/DW

Imam A. ya bayyana cewa irin wannan barazanar da tsoratarwar suna mummunan tasiri a fannin gudanar da addini yadda ya kamata. A yanzu haka ma dai, adadin mahalarta sallar Jumma'a a masallacinsa ya ragu matuka, inda maimakon masallata 100 ake samun 10 kacal a loakcin sauke farali. Matasan Musulmi sun kasance a sahun wadanda ba sa samun kwanciyar hankali kwata-kwata. 'Yan sanda na ci gaba da bincike domin gano wadanda suke kai hari a kan masallacin, duk da cewa ana inganta matakan tsaro a kewayensa.

Rashin kai korafi daga Musulmi

Saman malamin addinin Musulumci ne da ya yi korafi  kan wasikun barazana da yake samu, inda ake gayyatarsa da ya koma kasarsa ta asali. Yayin da daga lokaci zuwa lokaci, ake tura masa da majigi da ke batanci ga annabi Muhammad SAAW. Sai dai Daniel Höltgen ya ce Musulmi ba sa ba da rahoton korafi kan kiyayya da kyama da ake nuna musu, walau don ba su san inda za su shigar da kara ba ko kuma suna ganin cewa babu abin da zai canza. Wakilin majalisar da ke yaki da kyama ga Yahudawa da Musulmi a Turai ya yi tir game da rashin hukunta masu yada wannnan dabi'a ta Internet. 

Aiman A. Mazyek Vorsitzender des Zentralrats der Muslime in Deutschland (ZMD)
Shugaban majalisar koli ta addinin Musulumci a Jamus, Aiman A. MazyekHoto: Christoph Strack/DW

Höltgen ya tunatar da cewa wadanda suka kai hari a Halle a 2019 sun watsa abin da suke aikatawa a kafar Internet. Sai dai daga bisani dokar EU game da ayyukan kafofin sada zumunta, wanda aka kafa a karshen 2020 ta sanya alhakin irin wadannan kalaman a wuyan kamfanonin Internet domin su rika hattara. Shugaban majalisar koli ta addinin Musulumci a Jamus Aiman ​​Mazyek ya ce, matsalar kiyayya ga Musulmi wani jaririn abu ne, amma yana "karuwa matika gaya" a cikin 'yan shekarun nan. A cikin Jamus kawai akwai laifuka sama da 1000 da aka aikata a cikin shekarar 2020, ciki har da hare-hare 150 a kan masallatai. Ya yi fatan ganin cewar binciken da majalisar Tarayyar Turai ke yi, zai bayar da kwarin gwiwa domin daukar mataki kan wannan kiyayya.