Mutane 10 sun mutu a wani hari a Mogadishu
March 1, 2019Akalla mutane goma sun rasa rayukansu a Mogadishu na Somaliya lokacin da wata mota makare da bama-bamai ta tarwatse a kusa da wani kasaitaccen otal da ke tsakiyar birnin. Sannan rahotannin sun bayyana cewa wani mai fafutuka da makamai na musayar wuta da dakarun gwamnatin kasar ta Somaliya a yanzu haka.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan ranar Jumma'a, kungiyar al Shabaab ta yi ikirarin kaddamar da hare-haren a kan jami'an tsaro. Sai dai hukumomi sun bayyana cewar adadin wadanda suka rasu na iya karuwa, saboda ana ci gaba da tono gawarwakin da ke binne a baraguzan ginin otal din na al-Mukarama.
Duk da cewa an kori 'yan al shabaab daga Mogadishu a shekara ta 2011, amma har yanzu wasu yankuna na karkarar Somaliya na karkashin ikonsu. Kuma sun sha alwashin ganin bayan gwamnatin Somaliya wacce ke samun goyon bayan kasashen duniya.