1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane kusan dubu da ɗari shida aka ce sun halaka sakamakon girgizar ƙasar Japan

March 12, 2011

Girgizar ƙasa da kuma ambaliyar ruwa ta tsunami a ƙasar Japan sun haifar da damuwa a game da ɓarna a tashar makamashin nukiliya ta Fukushima mai tazarar kilomita metan da hamsin daga Tokyo

https://p.dw.com/p/10Y4Z
Ambaliyar ruwa ta tsunami ta yi mummunar ɓarna a ƙasar JapanHoto: dapd

Ana ci gaba da zaman makoki a ƙasar Japan, kana Japanawa na ƙokarin tunƙarar ta'adin daya afku a yankin arewa maso yammacin tekun ƙasar. Wasu garuruwa da biranen dake yankin dai na fama da mummanar ambaliyar ruwa sakamakon girgizar ƙasar da ta afku ta ƙarƙashin teku a wannan Jumma'a. Girgizar ƙasar mai ƙarfin marki 8 da ɗigo tara dai, itace mafi tsanani tun sa'adda ƙasar ta Japan ta fara ajiye bayanai game da ƙarfin girgizar ƙasa. A halin da ake ciki kuma gwamnatin ƙasar ta Japan ta yi kashedin cewar akwai bututun da suka huje a wasu cibiyoyin nukiliyar ta guda biyu. Tashoshin nukilyar da matsalar ta shafa dai sun haɗa da Fukushima ta ɗaya da ta biyu, waɗanda dukkanin su biyu ke da mazauni a yankin arewa maso gabashin ƙasar - mai tazarar kilomita 250 daga Tokyo babban birnin ƙasar. Firaministan Japan Naoto Kan ya bayar da umarnin faɗaɗa aikin sauyawa mutanen dake zaune kusa da cibiyoyin wuraren zama da kimanin kilimita goma maimakon kilomita uku, wanda ke nuna cewar kimanin mutane dubu 45 ne za'a sauya wa matsugunai daga yankunan da suka fi fuskantar hatsari. Girgizar ƙasa tare da ambaliyar ruwa ta tsunami dai sun lalata birnin Sendai dake arewa maso yammacin Japan, inda wani jami'in ɗan sanda ya ce tuni aka gano gawarwakin da adadin su ya kai tsakanin 200 zuwa 300 daga teku. An dai ƙiyasce cewar yawan mutanen da suka mutu zai kai dubu ɗaya da ɗari shida. Kuma tuni aka kwashe mutane dubu ɗari biyu daga yankin dake kewayen tashar nukilyar ta Fukushima.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Ahmad Tijani Lawal