Mutane shida sun mutu a cikin harin Bam a Somaliya
July 26, 2015A ƙasar Somaliya aƙalla mutane shida akasarinsu jami'an tsaro sun halaka a sakamakon wani hari da aka kai a yammacin Lahadin nan a babban birnin ƙasar Mogadiscio. Hukumomin 'yan sanda ta birnin na Mogadiscio sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewar an kai harin ne da wata mota shaƙe da ababe masu fashewa a Hotel Jazeera wacce ga al'ada mambobin gwamnatin ƙasar ta Somaliya dama jami'an diplomasiyyar ƙasashen ketare da ke a ƙasar dama kuma 'yan yawan buɗe ido suke zama cikinta
Tuni dai Ƙungiyar Alshebab ta ɗauki alhakin kai wannan hari inda kakakinta Cheikh Abdiasis Abu Musab ya ce sun kai harin ne a kan sojojin rundunar tsaro ta Afirka ta Amisom dama mambobin gwamnatin ƙasar ta Somaliya a matsayin martani ga jerin hare-haren da suke ta ƙaddamarwa a kan mayakan Ƙungiyar ta Alshebab.