Mutane 70 sun makale a karkashin Otel da ya rufta a China
March 7, 2020Talla
Kimanin mutane 70 suka makale a karkashin baraguzan wani Otel da ya rufta a gabashin kasar China da yammacin Asabar. Dama dai ana amfani da Otel din ne wajen killace wadanda ke fama da cutar nan ta Coronavirus.
Wasu hotunan bidiyo sun nuno masu aikin ceto na Otel din wanda ke a birnin Quanzhou, suna kokarin zakulo mutane inda a yanzu ake da sama da mutum 30 da aka samu da rai.
Hukumomin yankin dai ba su kai ga cewa uffan kan lamarin ba, musamman ma bayanai kan adadin wadanda suka mutu.
Batun rugujewar gine-gine dai ba sabon abu ba ne a China, abin da ke da alaka da saurin girma da kasar ke yi, inda wasu ke amfani da hakan wajen saba ka'idodjin gini.