1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahara sun kashe sojojin Burkina Faso

Abdul-raheem Hassan
August 19, 2021

Sabon harin ta'addanci ya hallaka fararen hula 30, jami’an tsaro 14 tare da jikkata mutane 19 a arewacin kasar da ke kan iyaka da kasar Mali.

https://p.dw.com/p/3z9Ga
Symbolbild I Sicherheitsbeamte Burkina Faso
Hoto: Ahmed Ouoba/AFP/Getty Images

Rahotanni na cewa 'yan ta'adda uku sun mutu a lokacin musanyar wuta da hukumomin tsaro. Shugaban kasar na Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku a fadin kasar.

Kasar Burkina Faso na cikin yankin Sahel da ke fama da barazanar kungiyoyi 'yan ta'adda masu alaka da al-Qaeda, sai dai hare-haren sun kara tsanananta ne daga 2015. Tun farko Faransa ta karfafa sojinta a yankin don cimma burin kasashen da ke yankin Sahel na kakkabe ta'addanci. Mutane da dama sun mutu sanadiyyar hare-haren akalla mutane miliyan daya da 200,00 sun yi hijira a cewar Majalisar Dinkin Duniya.