1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutuwar dakarun wanzar da zaman lafiya a Somaliya

October 21, 2011

Ƙungiyar Al-Shabaab ta ɗauki alhakin hallaka wasu dakarun wanzar da zaman lafiya na ƙungiyar tarayyar Afurka a Somaliya.

https://p.dw.com/p/12wIv
Sojojin gwamnatin Somaliya ke sintiri a titunan Mogadishu a ƙoƙarin wanzar da zaman lafiyaHoto: picture-alliance/dpa

Ƙungiyar Al-Shabaab a Somaliya ta baza kimanin gawawwaki 70 a babban birnin ƙasar wato Mogadishu waɗanda ta kira dakarun wanzar da zaman lafiya na ƙungiyar tarayyar Afurka ne waɗanda suka rasa rayukan su a filin daga. Kakakin ƙungiyar Sheikh Ali Mahmud Rage ya bayyanawa kamfanin dillancin labarun Faransa AFP cewa ƙungiyar ta ɗauki alhakin hallaka sojojin sama da 70. Idan har aka tabbatar da afkuwar hakan wannan zai zama kisan kiyashi mafi muni a ƙasar a tsukin shekaru huɗu. Shaidu dai sun tabbatar da cewa gawawwakin na nan jibge a yankin Alamada mai tazarar kilometa 18 daga Mogadishu wanda ke ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar, a ciki har da sojojin Burundi guda 63. Dakarun wanzar da zaman lafiya ƙungiyar tarayyar Afurka da ke Somaliya wato AMISOM da dakarun gwamnatin ƙasar sun yi ta ƙoƙarin kutsawa zuwa sauran wuraren da ƙungiyar ke da ƙarfi a Mogadishu bayan da suka ƙaurace wa mahimman wurare a babban birnin a watan Agustan da ya gabata.

Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita: Mohammad Nasiru Awal