1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan Jaridun Jamus

April 15, 2022

Jaridun Jamus sun yi nazari kan ziyarar Baerbock a Mali da matsalolin ambaliyar ruwa da boren kyamar baki a Afirka ta Kudu da kuma hukunci kan kisan Sankara.

https://p.dw.com/p/4A0QO
Außenministerin Annalena Baerbock besucht Mali
Hoto: Florian Gaertner/Auswärtiges Amt/Photothek/dpa/picture alliance

Jaridar Süddeutsche Zeitung da Neues Deutschland da die Welt da die Tageszeitung duk sun yi tsokaci kan batun inda suka ambato Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock tana kiran tabbatar da kwakwaran kudiri na wanzuwar dimukuradiyya a Mali. Tana mai cewa a halin da ake ciki har yanzu babu tabbas yadda za a cimma wannan kudiri da gwamnatin rikon kwarya a Bamako. 

Annalena Baerbock ba ta boye ba, wajen baiyana hakan ga shugaban gwamnatin rikon kwarya Assimi Goita a ganawarta da shi a ranar Laraba da ta gabata, a yayin ziyarar da ta kai Bamako. Ta ce, dole ne a sami sauyin manufa domin cigaban kawancen hadin kai da kasar ta Mali.

Baerbock ta kuma jaddada kudirin rundunar bada horo ta tarayyar Turai EUTM na son ci gaba da taimaka wa Mali shawo kan matsaloli da suka yi wa kasar dabaibayi. Kasashe 24 ne na tarayyar Turai suke cikin rundunar bada horon a Mali tun shekarar 2013 musamman wajen horar da sojojin Mali yaki da kungiyoyin jihadi da kuma taimakawa tabbatar da tsaro da zaman lafiya a kasar. A ranar 31 ga watan Mayu ne, majalisar dokokin Jamus za ta yanke hukunci a kan makomar aikin sojojin Jamus a Mali.

Überschwemmung in Südafrika
Ta'asar ambaliyar ruwa a Kwazulu-NatalHoto: AP/picture alliance

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi sharhi ne kan ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya hallaka mutane da dama a Afirka ta Kudu. Jaridar ta ce, mamakon ruwan sama da aka kwashe kwana da kwanaki ana tafkawa a gundumar Kwa-Zulu-Natal da ke gabar kogi ya hallaka mutane da dama. Akalla mutane 253 aka gano kawo yanzu sun rasu a cewar ministan lafiya Nomagugu Sumelane-Zulu. Shugaban Afirka ta Kudun Cyril Ramaphosa ya ziyarci yankin da aka yi ambaliyar inda ya jajanta musu tare da ba su tabbacin taimakon gwamnati.

Südafrika Proteste gegen Arbeitsmigranten
Boren kin jinin baki a Afirka ta KuduHoto: Guillem Sartorio/AFP

Taimakawa juna ba fada da juna ba. Wannan shi ne taken sharhin jaridar die Tageszeitung. Jaridar ta yi tsokaci kan tarzomar wariyar jinsi da aka yi wa lakabi da "Operation Dudula" a kan baki 'yan cirani. Ministan 'yan sanda Bheki Cele ya ce, abin takaici ne yadda aka afka wa shaguna da kantunan 'yan cirani a birnin Johannesburg inda ya yi alkawarin tura karin daruruwan 'yan sanda domin tabbatar da tsaro da kariyar bakin 'yan cirani. Sai da a cewar Elvis Nyathi wani dan cirani daga kasar Zimbabuwe ikrarin 'yan sandan na zama ihu bayan hari domin sun zo a makare bayan an tafka ta'asa.

Bildkombo Blaise Compaore und Thomas Sankara
Blaise Compaore da Thomas Sankara

A nata sharhin jaridar Neue Zürcher Zeitung cewa ta yi, shari'ar kisan gwarzon juyin juya-halin Burkina Faso ya kammala da daurin rai da rai ga tsohon Shugaba Compaore. Jaridar ta ce, hukuncin mai tsanani a shari'ar da ta dauki hankali game da kisan tsohon shugaban Burkina Faso Thomas Sankara da aka yi wa kisan gilla wanda har yanzu matasan Afirka suke tunawa da shi a matsayin jan gwarzo. A ranar Laraba da ta gabata, wata kotun soji a Ouagadougou babban birnin kasar, ta baiyana hukuncin daurin rai da rai akan Blaise Compaore mutumin da ya gaji Sankara. Alkalan suka ce an same shi da hannu a kisan kamar yadda bincike ya tabbatar.

Sankara tare da wasu mukarrabansa sojoji suka harbe a Ouagadougou a ranar 15 ga watan Oktoba 1987. A wannan lokaci ne kuma Compaore ya karbi mulki har zuwa shekarar 2014 da aka yi masa juyin mulki. Tun daga wannan lokaci ya ke gudun hijira a makwabciyar kasar Ivory Coast inda ya samu takardar zama dan kasar.

Jama'a da dama a Burkina Faso sun yi murna da hukunci inda uwargidan marigayin Mariam Sankara ta ce, ta gamsu da hukuncin kuma a yanzu jama'a za su fahimci Sankara mutum ne na kwarai dan kishin kasa mai nagarta.