Najeriya: Boss Mustapha ya fara aiki
November 1, 2017Rantsar da Boss Mustapha a matsayin sabon sakataren gwamnati don maye Babacir Lawal dai ya kawo karshen caccakar Buhari da ake yi game da rashin daukar mataki kan sakamakon binciken da aka mika masa na badakala ta cin hanci da ake zargin Babacir da aikatawa. To sai dai duk da cewar wannan ta, a share guda sama da kashi 50 cikin dari na mukamai sama da dubu shidda da gwamnatin ke fatan nadawa dai har yanzu suna hannun jam'iyar adawa ta PDP lamarin da wasu 'yan jam'iyyar APC ke nuna takaici a kai to amma dai gwamnatin na cewar za ta duba wannan abu don dauakr matakin da ya dace yayin da shi sabon sakataren gwamnatin Najeriyar ke cewa "har yanzu ba a makara ba a kokarin da jam'iyar APC ke yi na sauke nauyi da alkawuranta da nufin hada kan yayan jam'iyyar."
Talakawa dama ragowar mabiya a cikin sauyin na gaza kaiwa ga tabbatar da ta zarce ga shugaban kasar dai na nuna alamar jan aikin da ke gaban mazauna fadan gwamnatin. To sai dai kuma a fadar Bindow Umaru Jibrilla da ke zaman gwamnan Adamawa "nadin Boss Gida Mustapha a matsayin sabon sakataren gwamnatin Najeriya zai tabbatar da sauyi." A yanzu dai abin jira a gani shi ne tasiri na matakai na gwamnatin APC wajen iya kaiwa ga tabbatar da hadin kai a tsakanin jam'iyyar mai mulki ta APC da ke da burin tabbatar da dorewa a bisa mulki a kasar.