Najeriya: Sabuwar majalisar wadata kasa da abinci
March 26, 2018A wani abin da ke zaman sabon yunkuri na wadatar da kasa da abinci, Tarrayar Najeriya ta kafa wata sabuwar majalisar tabbatar da wadatar da abinci da ke da burin kawo karshen rikicin manoma da makiyaya da kuma kai kasar ya zuwa karatu na wadata a cikin hajjar ta abinci.
A jihar Benue dai kuma a fadar jami'ai na gwamnatin jihar an yi asarar kusan tan miliyan takwas na shinkafa, sakamakon rikicin makiyaya da manoman da ya kalli kauracewar kowa daga harkar noma a jihar.
A yayin kuma da su ma masunta da masu sana'ar noman a cikin tafkin Chadi suke fadin ta yi baki ta kuma lalace sakamakon yakin cikin kasar na ta'addanci da ya kalli kauracewa gonaki da ma wuraren yin su din.
Matsalolin kuma da gwamnatin ke kallon barazana ga kokari na wadatar da abincin da ke da tasiri ga rayuwa ta 'yan kasar.
Abin kuma da ya kai ga Abujar kaddamar da wata majalisar samar da abincin da ta kunshi shi kansa shugaban kasar da wasu gwamnonin jihohi guda shida game da manyan hafsoshi na tsaro da nufin kallon daukacin batun na abinci da ido na tsaro da kuma wadata shi tsakanin sassa na kasar.
Masalaha tsakanin manoma da makiyaya
Majalisar dai na da babban burin sasanta manoma da masu sana'ar kiwon game da kuma bullo da dabaru na ingantar harkokin noma a cikin zama na lafiya da karuwa ta arziki a tsakanin kowa.
Atiku Bagudu da ke zama gwamnan jihar Kebbi shi ne kuma mataimaki ga hukumar da ta tsara ganawa a kai a kai da kuma nazarin mafita a kokari na samar da abincin da ya ce akwaim kokari na girmama juna don samar da arziki da wadata.
Kokari na girgima juna da nufin samar da arziki, ko kuma rikicin 'yan haye da 'ya'yan gado dai matsalar ta fadace-fadace da ake ta'allakawa da siyasa ce ake yi wa kallon babbar barazana ga wadatar da kawuna da abincin.
Darius Ishaku shi ne gwamnan jihar Taraba da ke tsakiyar rigingimun da ke tashi da lafawa ya ce matsalar ta kama hanyar kaiwa ya zuwa tarihi tare da hukumar da ke zaman irinta ta farko.
Ya zuwa yanzu dai sabuwar kiddiddiga na nuna akalla mutane milliyan uku na fuskantar mummunan karanci na abinci a Tarrayar Najeriyar.