1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Nijar da Najeriya sun kashe 'yan ta'adda

Ramatu Garba Baba
May 30, 2023

Rundunar hadin gwiwar Najeriya da Nijar sun yi nasarar halaka akalla mayakan jihadi 55 a yayin wani samamen hadin gwiwa da suka kai mabuyarsu a garin Arege.

https://p.dw.com/p/4RxQm
An halaka mayakan ISWAP 55 a iyakar Najeriya da NijarHoto: Audu Ali Marte/AFP/Getty Images

Rundunar sojin Nijar ta ce ta yi nasarar halaka akalla mayakan jihadi hamsin da biyar a yayin wani samame na hadin gwiwa da ta kai da taimakon rundunar sojin Najeriya a mabuyar 'yan ta'addan ISWAP. Rundunar ta yi karin bayani da cewa, an kwashi kwanaki 22 ana kai farmakin kan mabuyar 'yan ta'adda a garin Arege a yankin Arewa maso gabashin Najeriya da ke kan iyaka da Nijar.

Kasashen biyu da ke fama da matsalar masu tayar da kayar baya sun kai samamen ne, don kara matsin lamba ga kungiyar da kuma yanke mata hanyoyin samun kayayyaki. Nijar na daga cikin kasashen yankin Sahel da ke fama da tashe-tashen hankula a sakamakon ayyukan 'yan ta'addan.