1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar:Kamen sojoji bayan yunkurin juyin mulki

Abdourahamane Hassane
April 1, 2021

Kura ta lafa a birnin Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar Nijar, bayan da rundunar tsaron fadar shugaban kasa ta yi nasarar murkushe wani yunkurin juyin mulki da wasu sojoji suka yi.

https://p.dw.com/p/3rUvm
Niger / Putsch / Niamey
Hoto: AP

Tuni dai wasu masu fafutukar kare dimukuradiyya a Nijar din, suka fara nuna damuwarsu game da wannan yunkuri nakifar da gwamnatin shugaba mai shirin barin gado Mahamadou Issoufou ta hanyar juyin mulki, abin da ka iya mayar da dimukuradiyyar kasar baya.