1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijeriya: Mataki kan kiyaye dokar hanya

Salissou Boukari
August 29, 2017

Yawaitar hadaruda da ake samu a bisa hanyoyin tarayyar Najeriya har ma a cikin birane da kuma karya dokokin hanya, sun sanya hukumar kula da dokokin hanya daukan matakin ladabtarwa.

https://p.dw.com/p/2j1VV
Nigeria Stau Afrika
Zirga-zirgan ababen hawa a birnin Lagos na NajeriyaHoto: Getty Images/P.U.Ekpei

 Wannan sabon tsari da hukumar kula da dokokin hanya ta Najeriyar ta bullo da shi da nufin sauya halayyar ‘yan Najeriya masu karya dokokin hanya a kasar, na zama mataki na baya-baya nan da ke kokarin ladabtarwa da ma canza yadda ‘yan kasar ke tuki barkatai. Laifukan guda biyar da suka hada da kin tsayawa a lokacin da wutar da ke bada hannu ta tsayar da direba, da tukin ganganci da kuma bin hannu da bai dace ba mai tuki ya bi na daga cikin laifukan da za su sanya a tura mutun asibiti don bincikar kwakwalwarsa.

Tuni dai an kama masu tuki sama da dubu biyu a Abuja, yayin da sama da 200 aka tura su asibiti don yin wannan gwaji.  Ko me ya sa suka bullo da wannan doka bayan can da akwai wacce ake amfani da ita. Mr Jerry Imeh na daya daga cikin wadanda suka je asibiti wajen gwajin, ko ya yaji?

Tansania Muhimbili National Hospital in Daressalam
Likita na binciken lafiya a babban asibitiHoto: DW/R. Velton

"Gaskiya ban ji dadi ba domin nasan banni da tabin hankali amma ala tilas sai da naje na yi gwaji a kan tunanin hankalina, na iske ‘yan Najeriya da dama a asibiti su na korafi. Amma nasan wannan ya yi tasiri domin ba zan sake amsa waya ina tuki ba, da zarar wayata ta buga zan tsaya tukuna, kai na fa wahala''

Ga alamu dai sannu a hankali masu tuki sun soma shiga taitayinsu ganin yadda ake tilasta mu su yin wannan gwaji na auna kaifin hankalin mutun, domin kuwa duk wanda ya fuskanci wannan gwaji na yin taka tsantsan wajen kiyaye dokokin tuki, sannan kuma ya kasance ganau ba jiyau ba ga sauran jama'a da ke da irin wadannan halaye.