1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan cirani sun awana shekara a Hamada Tenere

Abdourahamane Hassane
April 2, 2020

Hukumar kaura ta duniya OIM ta ce ta ceto 'yan cirani sama 250 kusa da Madama a arewacin Nijar kan iyaka da Libiya cikin hamada Tenere. 

https://p.dw.com/p/3aNnL
Niger Binnenflüchtlinge Flüchtlinge Vertriebene Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Abodou

Hukumar ta OIM ta ce yanzu haka ta killace 'yan ciranin har tsawon makwanni biyu domin tantance ko suna dauke da cutar Coronavirus. 'Yan ciranin wadanda suka galabaita cikin hamada an ganosu tun makwannin biyu da suka wuce cikin hamadar. Daga cikinsu 104 'yan Najeriya, 53 'yan Ghana, sai 34 'yan Burkina Faso har da jariri a ciki a kan hanyarsu ta zuwa Turai ta barauniyar hanya.