1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar fahimta tsakanin Amirka da Rasha

Abdullahi Tanko Bala
January 13, 2022

Babban taron duniya kan tsaro da ya gudana a Vienna ya bukaci hada kan Rasha da Amirka da kawayensu na Tarayyar Turai domin samun tattaunawa ta fahimtar juna.

https://p.dw.com/p/45VZO
Österreich | OSZE-Sitzung im Zeichen der Krisendiplomatie mit Russland
Hoto: Alexey Vitvitsky/Sputnik/dpa/picture alliance

Kungiyar kawancen tsaro da raya cigaba a nahiyar turai OSCE ta na fatan kwantar da hankula a rikicin kan iyaka na kasar Ukraine inda Rasha ta jibge dakarun sojinta masu yawa.

Poland ta fara gabatar da mukala inda ta yi kashedin cewa akwai hadarin barkewar yaki a yankin kasashen kungiyar OSCE kuma lamarin ya yi kamari a wannan karon fiye da sauran lokuta shekaru 30 da suka gabata.

Ministan harkokin wajen Poland Zbigniew Rau ya shaidawa mahalarta taron a babban birnin Austria cewa akwai bukatar tabbatar da hadin kai da fahimtar juna a tsakanin kasashe.