Putin ya cika shekaru 25 kan mulki
December 31, 2024Za a iya cewa an faro tafiyar a watan Agustan shekarar ta1999 lokacin da aka nada Vladimir Putin a matsayin firaministan Tarayyar Rasha. Daga bisani Putin a jajiberin shekarar ta1999 lokacin da duniya take kokarin shiga sabuwar shekara ta 2000 kuma sabon karni, ya gaji Shugaba Boris Yeltsin na Rasha wanda yake fama da rashin lafiya kuma tun lokacin yake taka rawa a siyasar duniya. A lokacin ya zama mai aiwatar da sauye-sauye sakamakon matsalolin da Rasha ta fuskanta a shekarun 1990.
A shekara ta 2001 Shugaba George W Bush na Amurka na lokacin ya kira Putin a matsayin wanda za a yarda da shi kuma mai kaifi daya, bayan ganawar da suka yi lokacin tsaron kungiyar tsaron NATO da Bush ya jagoranta. A watan Satumba na shekara ta 2001 Vladimir Putin ya ba da damar aiki tare da Turai a bangaren tsaro lokacin da ya gabatar da jawabi a gaban majalisar dokokin Jamus ta Bundestag. Inda ya saka ayar tambaya game da jagorancin kasashen yamma.Kungiyar kasashen Tarayyar Turai da Rasha sun amince da tsare-tsare da dama har kungiyarNATO ta bude ofishi a birnin Moscow fadar gwamnatin Rasha, yayin da Rasha ta tura da wakili zuwa kungiyar NATO a birnin Brussels na Beljiyam. Firaminista Viktor Orban na Hangari, yana cikin masu dasawa da Shugaba Putin, wanda ya kare matakin cewa Rasha tana karkashin kama-karya. Shi ma tsohon shugaban gwamnatin Jamus, Gerhard Schröder ya sha nuna jinjina ga Putin, duk yana ganin yadda sannu a hankali aka kawar da 'yan adawa a kasar da kafofin yada labarai masu zaman kansu. Schröder yana da tasiri a bangaren kamfanonin makamashin Rasha.
A lokacin taron tsaro a birnin Munich na Jamus a shekara ta 2006 Vladimir Putin ya nuna rashin jin dadi yadda kasashen Yamma suka gaza amincewa da Rasha a matsayin daya daga cikin masu fada aji a duniya. Ya kuma zargi kungiyar tsaronNATO da karya alkawuran da ta dauka. Alkawarin cewa kar kungiyar NATO ta fadada zuwa iyakar Rasha an kawar da kai. Amma a shekarar 1997 Rasha ta amince da batun fadada kungiyar tsaron NATO. A watan Agustan shekara ta 2008 Putin ya nuna matsayin Rasha wajen yaki a Georgia tare da kwace yankunan kudancin Ossetia and Abkhazia.
A shekara ta 2014 an samu bore a Ukraine abin da ya kawo karshen shugaba mai goyon bayan Rasha. Putin ya kai farmaki kan Ukraine daga bisani inda ya kwace tsibirin Cremea lamarin da ya saba dokokin kasashen duniya. A watan Maris na shekara ta 2022, Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya kaddamar da yaki kan kasar Ukrane. Shugaba Joe Biden na Amurka ya dauki Putin a matsayin dan kama-karya wanda ya aikata laifukan yaki. Shekaru 25 bayan zuwan Putin kan madafun iko an shiga sabon yanayin rige-rigen sayen makamai.