Ranar Hausa: Kokarin inganta Hausa a aikin jarida
August 26, 2022Jamhuriyar Nijar ta bi a wannan Juma'a sahun wasu kasashen duniya wajen raya Ranar Hausa ta duniya da ake yi a duk ranar 26 ga watan Agusta na kowace shekara. Masana harshen Hausa a kasar ne dai suka shirya gagarumin taro a birnin Yamai domin tulawar halin da harshen ke ciki a duniya.
Rawar da kafafen yada labarai na gida da na ketare ke takawa wajen yadawa da kuma bunkasa harshen Hausa na daga cikin muhimman makalolin da aka gabatar a wajen wannan biki. Tsohon dan jarida Malam Idi Baraou shi ne ya gabatar da mukala kan wannan maudu'i.
''Yadda a duniya ake amfani da harshen Hausa a kasashe wajen 45 daga cikin 32 a Afirka, shi ya sa aikin jarida ke bayar da babbar gudunmawa wajen bunkasa da yada harshen Hausa da al'addun Bahaushe da ma rayuwarsa baki daya'' Malam Baraou ya shaida wa DW Hausa.
'Yan jarida masu yawa da sauran ma'abota sauraran shirye-shiyen Hausa a kafafen yada labarai ne dai suka halarci bikin, sun kuma bayyana abubuwan da suke alfahari da su da kuma wadanda suke ganin na bukatar gyara a cikin tafiyar da harshen Hausa a kafafen yada labarai.
''A fannin gidajen radiyo na kasa da kasa, wani abin da ke bukatar gyara shi ne wasu wakilansu daga wasu kasashe sukan amfani da karkatacciyar Hausa ko ta wani yanki wadda ba kowa ke gane ta ba maimakon su yi amfani da ingantacciyar Hausa wadda ta zamo gama-gari da duk Bahaushe a ko'ina yake zai fahimta'' in ji daya daga cikin masu sauraron radiyo a Nijar.
Wasu alkaluma dai sun nunar da cewa harshen Hausa wanda mutane sama da miliyan 200 ke amfani da shi a yau a duniya na a matsayin na 11 daga cikin jerin harsunan duniya kimanin dubu bakwai. A Nijar kimanin kaso 50 daga cikin 100 na miliyan 24 na al'ummar kasar Hausawa ne amma kuma akwai kusan kaso 70 daga cikin 100 na al'ummar kasar da ke magana da wannan harshe a harkokinsu na yau da kullum.