Bikin ranar masoya ta duniya
February 14, 2023Talla
A fadin duniya matasa suna ranar da aka kebe domin masoya inda masoyan ke yi wa juna kautattuka tare da raya daren .Lokacin da sauran yankunan kasar ta Jamhuriyar Nijer ke wannan biki haka batun yake a jihar Tahoua inda matasa da dama ke wannan bikin na masoya inda wasu daga ciki ke sayen wasu abubuwa kawatan masoya.
Babu shakka a makamancin wannan lokacin na bikin Saint-Valentin masu shaguna na samun bunkasar sana'o'in musamman masu shagunan kayan kawa. To saidai kuma a dai wani bangaren wasu daga cikin matasan na fahimtar bikin ne da wata manufa ta daban musamman ganin wasu na shiga mawuyacin hali domin samun abin da za su bayar da sunan soyayya.