Ranar nada shugaban rikon kwarya a Burkina
October 8, 2022Wata doka da aka karanta a gidan talbijin na kasar RTB ta nunar da cewar tattaunawar da za a yi a birnin Ouagadougou za ta samu halartar 'yan siyasa da shugabannin kungiyoyin farar hula na Burkina Faso domin amincewa da yarjejeniyar mika mulki.
Dama dai shugaban Burkina Faso da aka nada a hukumance a ranar Laraba da ta gabata Kyaftin Ibrahim Traore, ya ba da tabbacin hanzarta mika mulki bayan da ya hambarar da Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba, wanda shi ma ya kifar da zababben shugaban kasar Roch Marc Christian Kaboré biyo bayan tabarbarewar tsaro.
A cikin 'yan watannin baya-bayannan dai, hare-hare sun yawaita a arewaci da gabashin kasar Burkina Faso, inda a yanzu haka garuruwa da dama ke karkashin ikon masu ikirarin jihadi.